Ronaldo zai gana da Ten Hag kan makomarsa a Man United

Cristiano Ronaldo

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Cristiano Ronaldo zai gana da kociyan Manchester United, Erik ten Hag domin su tattauna kan makomarsa a kungiyar.

Kyaftin din tawagar Portugal, mai shekara 37, na bukatar United ta bar shi ya bar kungiyar a kakar nan.

Bai je wasannin sada zumunta da ta yi a Thailand da Australia ba a watannan, saboda wasu dalilai da suka shafi iyalinsa.

Har yanzu bai yi atisaye tare da 'yan wasan United ba, amma yanzu ya koma Old Trafford.

Tun a baya kociyan United, Erik ten Hag ya sanar cewar Ronaldo ba wanda za su sayar bana a kakar nan.

Ronaldo ya koma Old Trafford da taka leda a bara, bayan da ya kammala wasa a Real Madrid da kuma Juventus.

Cristiano Ronaldo

Asalin hoton, Getty Images

Rashin atisaye tare da 'yan wasan United da Ronaldo bai yi ba, ya sa ake ta rade-radin makomar kyaftin din Portugal a bana a Old Trafford.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Sai dai kuma dan wasan ya ci gaba da motsa jiki a hedikwatar tawagar kwallon kafa ta Portugal.

Ronaldo shi ne kan gaba a ci wa United kwallo a kakar da ta wuce - na uku a yawan zura kwallo a raga a gasar Premier League, sai dai United ta kasa samun gurbin Champions League da za a yi a kakar nan.

United ta kare a mataki na shida a teburin babbar gasar tamaula ta Ingila, za ta buga Europa League a bana kenan.

Hakan ya sa da kyar ne idan Ronaldo zai amince ya buga Europa maimakon Champions League, duk da saura kaka daya kwantiaginsa ya kare a United.

A farkon watan nan Chelsea ta ce ta janye daga fatan sayen Ronaldo, wanda aka yi ta alakanta shi da Bayern Munich da kuma Atletico Madrid.

An fahimci cewar United ba ta shirya sayar da Ronaldo ba kawo yanzu.

United za ta kara da Atletico Madrid a Norway ranar Asabar daga nan ta koma Old Trafford don buga wasan sada zumunta da Rayo Vallecano a Old Trafford ranar Lahadi.

Za ta fara wasan farko a kakar bana a Premier League a gida da karbar bakuncin

Brighton ranar 7 ga watan Agusta.