Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Manyan bayanan sirri uku kan shirin Amurka na kai wa mayaƙan Houthi hari a Yemen
- Marubuci, Bernd Debusmann Jr
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, White House
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 4
Mujallar Atlantic ta wallafa wata tattaunawa da wasu manyan jami'an tsaron Amurka suka yi kan kai hare-hare ta sama a Yemen.
Wani zauren sada zumunta na Signal ya yi kuskuren saka babban editan Mujallar Jeffrey Goldberg a ciki, wanda kuma ke ɗauke da manyan jami'ai.
Bayan wallafa wasu daga cikin bayanai kan kai harin a farko, ya yanke shawarar wallafa sauran bayanai a ranar Laraba - bayan da manyan jami'ai suka hakikance cewa babu wasu bayanan sirri da aka yaɗa a zauren.
Waɗannan bayanai "sun janyo mun yi imanin cewa ya kamata mutane su kalli sakonnin domin su yanke shawara da kansu," kamar yadda Goldberg ya rubuta.
Ga wasu uku daga cikin sakonnin da muka yi bayani a kai.
Lokacin kai harin
Waɗannan sakonni sun fito cikakkun bayanai kan shirin sojojin Amurka na kai hare-hare ta sama a Yemen - wanda aka kwatanta "babban shiri", abin da ke nufin samar da jerin jirage masu saukar ungulu da makamai da kuma tattara na'urorin bayanan sirri domin kaddamar da harin.
"Batun da ya sa ba a bayyana sakonnin a matsayin na sirri ba a lokacin shi ne don ba su fito ba," in ji Glenn Gerstell, tsohon janar a hukumar tsaron Amurka, kamar yadda ya faɗa wa BBC.
Ya ƙara da cewa bayan fitar sakonnin, sun fita daga tsarin na sirri - amma duk wani yunkuri na sojojin Amurka wajen kai hari zai zamanto sirri a lokacin da a ce ba a yaɗa sakonnin ba.
Saƙonnin daga Hegseth sun lura da lokacin da aka tsara jirgin F-18 zai kai harin, da kuma lokacin da za a kai hare-hare da kuma daidai karfe nawa zai fi.
A wannan yanayi, "haddasa wa" yana nufin abubuwa da za a shirya waɗanda dole ne a yarda da su kafin a tura makamai. Zai iya zama wani wuri na tsara abubuwa, kamar hasken wayar hannu.
Ana ɗaukar wannan a matsayin bayanan sirri masu muhimmanci.
Philip Ingram, wani tsohon jami'in leƙen asiri na soji da ke aiki a rundunar sojin Birtaniya, ya shaida wa BBC cewa irin waɗannan bayanai "suna shiga cikin abin da ya kamata a ɓoye kuma da ya kasance na sirri".
Ya ƙara da cewa "Kuna iya yin shiri a kusan inda jirgin zai fito."
Kafin bayyanar tattaunawar, fadar White House da wasu jami'an Amurka sun yi iƙirarin cewa wannan bayanin ba yana nufin "shirin yaki" bane.
A cikin wani sako a shafin X, Hegseth ya ce: "Mujallar Atlantic ta fitar bayanai kan shirin kai harin kuma waɗannan" tsare-tsare sun haɗa da: Babu sunaye. Babu wurare. Babu hanyoyi kuma babu tushe. "
'Mai sarrafa makamai masu linzami'
A wannan ɓangare na tattaunawar a zauren sada zumuntar, mai ba da shawara kan harkar tsaro Mike Waltz ya yi ƙarin haske kan yunkurin kai harin.
Waltz ya bayyana cewa wurin da aka yi niyyar fara kai harin ya ruguje, kuma tun da farko sojojin Amurka sun gano wurin - wani ɗan Houthi mai harba makamin linzami" - lokacin da yake shiga ginin, wanda aka yi imanin gidan budurwarsa ce.
A cikin sakonsa, Waltz ya taya Pete murna - yana nufi ga Hegseth, da kuma masu tattara bayanan sirri da Michael Kurilla, Janar ɗin sojojin Amurka wanda ke kula da babban kwamandan wata rundunar yaki a Gabas ta Tsakiya da sassan Tsakiya da Kudancin Asiya.
Saƙonnin ba su bayyana yadda aka bi diddigin inda aka kai hari ba.
Wani kwararre kan soji da BBC ta tuntuɓa - amma wanda ya buƙaci a sakaya sunansa - ya ba da shawarar cewa za a iya amfani da hanyoyin jiragen sama, karfin bin diddigin fasaha ko bayanan sirri - wajen gano haka.
Aƙalla mutane 53 ne suka mutu a farkon harin da Amurka ta kai kan mayakan Houthi a Yemen, wanda ya faɗa kan shingaye sama da 30 da suka haɗa da wuraren horo, da kayayyakin aikin jirage marasa matuka, da wuraren ƙera makamai da wuraren ajiya da kuma cibiyoyin sarrafawa, ciki har da wanda ma'aikatar tsaron Amurka ta Pentagon ta ce akwai kwararrun masu sarrafa jiragen kai hare-hare.
Ba a san wane shinge ne daga cikin abubuwan da Waltz ke nufi ba a tattaunawar.
Ayyukan hukumar leƙen asirin Amurka (CIA) a Yemen
Wasu bayanan sirri masu muhimmanci su ne sakonnin da suka fito daga wajen Joe Kent, tsohon jami'in ayyuka na soji wanda kuma shugaba Trump ya naɗa don ba shi muƙamin daraktan cibiyar daƙile ayyukan ta'addanci - sai dai ya kasa tsallake tantancewa.
A sakonsa, Kent ya bayyana cewa Isra'ila na kai nata hare-hare.
Sojojin Isra'ila sun sha kai hare-hare kan wuraren Houthi a Yemen tun bayan ɓarkewar yaƙi a Gaza, don mayar da martani kan hare-haren masu linzami da kuma na marasa matuki da ƴan Houthi suka kai mata don mara wa Hamas.
Hari na baya-bayan nan shi ne wanda aka kai ranar 19 da kuma 26 ga watan Disamban 2024.
A cewar Kent, gwamnatin Isra'ila na son sake samar da duk wani makami da ya kamata don ci gaba da kai farmaki, duk da cewa ya yi imanin batun ba wani abu bane.
Wasu sakonnin sirri sun biyo daga wajen darektan hukumar leƙen asirin Amurka John Ratcliffe, wanda ya ce Amurka "na shirye-shirye" don taimakawa a kai hari, amma jinkiri "ba zai janyo mummunan tasiri" ga ayyukan hukumar ba a Yemen.
"Ƙarin lokaci zai ba da damar gano wurare da za a fara bi don sanin jagorancin Houthi," kamar yanda ya rubuta.
Abin da ake nufi a nan shi ne amfani da jami'an leƙen asirin CIA da ke Yemen ko kuma fasahohi kamar jirage marasa matuki.
Mick Mulroy, tsohon mataimakin sakataren tsaro kuma tsohon jami'in CIA, ya ce sakon Ratcliffe na sirri ne sosai.
"Maganar gaskiya, ba mu son yaɗa ko faɗar inda CIA ta dosa," in ji shi.
Ratcliffe ya faɗa a zauren majalisar ƙasar ranar Laraba cewa bai yaɗa bayanan sirri ba.