Masu VAR da suka yi kuskure a wasan Liverpool za su yi rafli a makon nan

Premier League

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Darren England da Daniel Cook za su yi rafli a Premier League a makon nan a karon farko, tun bayan da suka yi kuskure a wasan Tottenham da Liverpool.

England da Cook sune suka kula da VAR, inda suka soke kwallon da Luis Diaz ya ci wa Liverpool da cewar ya yi satar gida.

Tottenham ce ta yi nasara da ci 2-1 a wasan gasar Premier League a wasan da aka bai wa 'yan wasan Liverpool biyu jan kati.

Daga lokacin aka dakatar da alkalan wasan Premier League, wadanda za su koma kan aiki a karshen makon nan.

Shi England zai yi zaman ko-ta-kwana a wasan Brentford da za ta karbi bakuncin Burnley ranar Asabar.

Shi kuwa Cook shi ne mataimakin alkalin wasan da Sheffield United za ta karbi bakuncin Manchester United ranar Asabar.

Michael Oliver shi ne zai busa wasan da Manchester United za ta ziyarci Bramall Lane.

A farkon watan nan, Oliver bai wa dan kwallon Manchester City, Mateo Kovacic jan kati ba, wanda ya yi wa kyaftin din Arsenal, Martin Odegaard keta.