Shin ɗaukar kofin FA nasara ce ga Guardiola?

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Crystal Palace da Manchester City za su buga wasan karshe a FA Cup ranar Asabar a Wembley.

Palace ba ta taɓa lashe FA Cup ba a tarihi, wadda ta yi rashin nasara a wasan ƙarshe a 2016 a hannun City.

City kuwa ba baƙuwar ɗaukar FA Cup ba ce, wadda ta lashe bakwai, bayan nan da yi ta biyu a gasar karo shida.

Manchester United ce ke riƙe da kofin gasar na bara da ta ɗauka, bayan nasara a kan Manchester City da ci 2-1.

Sai dai a kakar nan Palace tana ƙoƙari a FA Cup, wadda ta yi waje da Fulham a zagayen kwata fainal da cin Aston Villa 3-0 a daf da ƙarshe.

City ta samu zuwa wasan ƙarshen karo na uku a jere bayan nasara kan Nottingham Forest da 2-0.

Ƙungiyoyin sun kara sau biyu a bana a Premier League, inda suka tashi 2-2 a gidan Palace ranar Asabar 7 ga watan Disambar 2024.

A wasa na biyu kuwa City ce ta doke Palace 5-2 a Etihad ranar 7 ga watan Disambar 2025

Haka kuma ƙungiyar da Pep Guardiola ke jan ragama tana ta huɗu a teburin Premier League da maki 65, ita kuwa Palace mai maki 42 tana ta 12 a kan teburin.

Wasa biyu ya rage a Premier League a kakar nan, bayan da tuni Liverpool ta lashe kofin na 20 jimilla, iri ɗaya da yawan na Manchester United.

Manchester City ƙarƙashin Pep Guardiola ta mamaye kofuna a baya-bayan nan, wadda ta ɗauki Premier a bara kuma na huɗu a jere.

A ƙarƙashin kociyan ɗan ƙasar Sifaniya, City ta lashe FA Cup biyu da League Cup har da Champions League da Fifa Club Worl Cup da sauransu.

To sai dai Guardiola ya ci karo da koma-baya a wasannin da yake buga wa, wanda Real Madrid ta yi waje da shi a Champions League zagayen cike gurbi.

Haka kuma City ta yi ban kwana da Carabao Cup na bana a cikin watan Oktoba, bayan da Tottenham ta yi nasara 2-1.

Rabon da City ta fice daga cikin ƴan biyun farko a teburin Premier League tun kakar farko ta Guardiola a 2016/17.

Kenan kofin FA Cup shi ne kaɗai fatan da Guardiola ke yi na ɗauka a kakar nan, idan ba haka ba, City za ta kare ba tare da kofi koda na shayi ba.

City wadda za ta buga wasan ƙarshe a Premier da Fulham ranar 25 ga watan Mayu daga nan za ta kece raini da Wydad ta Morocco a Club World Cup ranar 18 ga watan Yuni a Philadelphia.

Oliver Glasner ya kai Crystal Palace wasan ƙarshe a FA Cup a karon farko tun bayan 2016, wanda ya yi nasara a kan Aston Villa 3-0 a daf da ƙarshe.

Kenan Palace za ta yi fatan lashe FA Cup a karon farko a tarihi a wasan da za ta fuskanci Manchester City ranar Asabar.

A ƙarshen mako, Palace ta je ta doke Tottenham 2-0, hakan ya sa ta ƙara samun maki ya zama 49 a Premier, saura wasa biyu ya rage mata a kakar nan.

Kenan ta yi kan-kan-kan a yawan haɗa maki da yawa a kaka biyu ta Glasner, kuma watakila ta kara samun wasu makin a wasan da za ta yi da Wolves da Liverpool.

Glasner na samun waɗannan nasarorin duk da cewar Bayern Munich ta saye fitatcen ɗan wasa Michael Olise.

Tuni kuma Palace ta sanar cewar Joel Ward zai bar ƙungiyar a ƙarshen kakar nan, bayn 13 da ya yi.

Ward, mai shekara 35, ya buga wasa 363 shi ne kan gaba a wannan ƙwazon har da fafatawa 305 a Premier League.

Ward ya koma Palace daga Portsmouth mai buga Championship a 2012-13.

Wasan da aka kara tsakanin Crystal Palace da Manchester City a FA Cup:

FA Cup ranar Asabar 28 ga wwatan Janairun 2017

  • Crystal Palace 0 - 3 Man City

FA Cup 03 Jan 1981

  • Man City 4 - 0 Crystal Palace

FA Cup Sa 20Feb 1926

  • Man City 11 - 4 Crystal Palace

FA Cup Sa 08Jan 1921

  • Crystal Palace 2 - 0 Man City

Jerin waɗanda ke kan gaba a yawan lashe FA Cup

Arsenal FC Arsenal FC 14

Manchester United Manchester United 13

Liverpool FC Liverpool FC 8

Chelsea FC Chelsea FC 8

Tottenham Hotspur Tottenham Hotspur 8

Manchester City Manchester City 7

Aston Villa Aston Villa 7

Newcastle United Newcastle United 6

Blackburn Rovers Blackburn Rovers 6

Everton FC Everton FC 5

West Bromwich Albion West Bromwich Albion 5

Wanderers FC (- 1887) Wanderers FC (- 1887) 5

Wolverhampton Wanderers Wolverhampton Wanderers 4

Bolton Wanderers Bolton Wanderers 4

Sheffield United Sheffield United 4

West Ham United West Ham United 3

Sheffield Wednesday Sheffield Wednesday 3

Portsmouth FC Portsmouth FC 2

Sunderland AFC Sunderland AFC 2

Nottingham Forest Nottingham Forest 2

Preston North End Preston North End 2

Bury FC Bury FC 2

Old Etonians FC Old Etonians FC 2

Leicester City Leicester City 1

Wigan Athletic Wigan Athletic 1

AFC Wimbledon AFC Wimbledon 1

Coventry City Coventry City 1

Ipswich Town Ipswich Town 1

Southampton FC Southampton FC 1

Leeds United Leeds United 1

Blackpool FC Blackpool FC 1

Charlton Athletic Charlton Athletic 1

Derby County Derby County 1

Cardiff City Cardiff City 1

Huddersfield Town Huddersfield Town 1

Burnley FC Burnley FC 1

Barnsley FC Barnsley FC 1

Bradford City Bradford City 1

Notts County Notts County 1

Blackburn Olympic FC (- 1889) Blackburn Olympic FC (- 1889) 1

Old Carthusians FC Old Carthusians FC 1

Clapham Rovers FC (- 1914) Clapham Rovers FC (- 1914) 1

Royal Engineers Royal Engineers 1

Oxford University Oxford University 1