Za mu nishaɗantar da magoya baya, amma ba za mu yi alƙawarin cin kofi ba - Brighton

Brighton

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Kocin ƙungiyar Brighton & Hove Albion, wadda aka fi sani da Brighton, Fabian Hurzeler ya ce za su yi duk mai yiwuwa wajen burge masu kallo da nishaɗantar da su, musamam magoya bayansu.

Sai dai ya ce duk da ƙoƙarin da za suke yi, ba zai iya yin alƙawarin za su iya cin wani kofi ba a kakar ta bana.

Kocin ya bayyana haka ne a taron ganawa da manema labarai, a lokacin da yake amsa tambaya ko yana da burin lashe kofuna a ƙungiyar.

A cewarsa, "da farko dai yana cikin burina. Zan so in yi duk abin da zan iya, kuma lallai zan so ƙungiyar ta zama wadda ta fi kowacce samun nasara. Aikin da ke gabana ke nan tare da haɗin gwiwar sauran ma'aikata da ƴanwasa.

"Mun yi alƙawarin cewa za mu yi duk mai yiwuwa wajen nuna ƙwarewa a taka leda domin mu nishaɗantar da magoya bayanmu a kullum, wannan shi ne abin da muke yi, kuma muke da burin ci gaba da yi. Amma za mu ga abin da zai faru a nan gaba."