Ahmed Musa ne ya lashe ƙyautar fitaccen ɗan wasa a karawa da Akwa United

Asalin hoton, Getty Images
Ahmed Musa ne ya lashe ƙyautar gwarzon ɗan wasa a karawar da Kano Pillars ta yi nasara a kan Akwa United 1-0 ranar Laraba a filin wasa na Sani Abacha a Kano.
Ɗan wasan na tawagar Super Eagles ya taka rawar da ta kai Pillars ta samu maki uku a wasan mako na 26 a babbar gasar tamaula ta Najeriya.
Ƙyaftin Rabi'u Ali ne ya ci ƙwallon a minti na 84 a bugun fenatiri na 10 a bana kenan, kuma na 131 a dukkan fafatawa a gasar.
Musa, ya taka rawar da ta kai marubuta labarin wasannin na jihar Kano suka fitar a matsayin, shi ne kan gaba a ƙwazo a karawar tsakanin Pillars da Akwa.
Tsohon ɗan wasan Leicester City da CSKA Moscow ya fara taka leda a Pillars duk da ba da shi aka fara kakar nan ba, wanda ya yi jinyar da bai buga karawa shida ba.
Duk da haka Musa ya ci ƙwallo shida yana da hannu a zura wasu ƙwallayen da sai masu gida ta ci a kakar nan.
A jawabinsa bayan tashi daga karawar, Musa ya ce zai ci gaba da taka rawar gani da Pillars za ta ci gaba da taka rawar gani a gasar - ya kara da cewar zai sa ƙwazo a wasa da Rangers a nan gaba.
Ya kuma gode da yadda magoya baya ke mara musu baya da gudunmuwar da suke bayar wa a dukkan wasannin Pillars.
Kawo yanzu Pillars ta yi wasa huɗu a jere ba tare da an doke ta ba, hakan ya sa ta koma ta shidan teburi da maki 39, bayan wasannin mako na 26.
Kano Pillars za ta karɓi bakuncin Enugu Rangers a wasan mako na 27 a filin wasa na Sani Abacha.












