Liverpool ta bayar da tazarar maki bakwai a teburin Premier

Salah

Asalin hoton, Reuters

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Liverpool ta doke Wolverhampton 2-1 a wasan mako na 25 a Premier League ranar Lahadi a Anfield, ta bayar da tazarar maki bakwai a teburi.

Luis Diaz ne ya fara ci wa Liverpool ƙwallo a minti na 15 da fara wasan, sai Mohamed Salah da ya ci na biyu a bugun fenariti tun kan hutu.

Ƙwallo na 28 da Salah ya ci a dukkan karawa a bana a Liverpool, kuma na 23 a babbar gasar tamaula ta Ingila ta kakar nan.

Haka kuma karo na 101 da Salah ya zura ƙwallo a raga a Premier League a Anfield, ya yi kan-kan-kan da Wayne Rooney da ya yi wannan bajintar a Old Trafford.

Waɗanda ke gabansu a wannan ƙwazon ya haɗa da Thiery Henry mai 114 a Highbury da Sergio Aguero a Etihad mai 106 a raga.

Trent Alexander-Arnold ya buga karawar kuma karo na 250 a Premier League, mai shekara 26 da kwana 132 ranar Asabar.

Hakan ya sa ya haura Steven Gerrard mai rike da tarihin a Liverpool mai karancin shekara da ya buga wasa da yawa a Premier a Disambar 2006.

Da wannan sakamakon Liverpool ta ci gaba ta jan ragamar teburin Premier League da tazarar maki bakwai tsakani da Arsenal ta biyu mai 53 da Nottingham Forest mai maki 47.

Kociyan Liverpool, Arne Slot ya yi nasara ta 24 daga wasa 28 a Premier League dacsauran gasa a kakar nan.

Liverpool za ta je Aston Villa ranar Laraba 19 ga watan Fabrairu, domin buga wasan gaba a Premier League.