Amfani shida da gurji ke yi ga jikin ɗan'adam

Asalin hoton, BBC Igbo
Gurji kayan lambu ne mai amfani sosai, cike da sinadarai masu gina jiki da kuma fa'ida ga lafiyar ɗan'adam.
Yayin da wasu ke yi wa gurji kallon yana ajin kayan ganyayyaki ne yayin da kuma wasu ke ganin yana cikin kayan ƴanƴan itace ne.
Amma gaskiyar magana ita ce, gurji yana cikin ajin kayan ganyayyaki ne saboda yana da iri a ciki - uma yana ɗauke da muhimman sinadarai kamar su bitamin A da K da C da potassium da calcium sannan yana ɗauke da harza, kamar yadda masana abinci suka bayyana.
Baya ga kasancewarsa abin amfani a abubuwa daban-daban, gurji na da matuƙar amfani ga lafiyar ɗanadam.
Ga wasu daga cikin amfanin gurji da masana suka bayyana:
Rage ciwon Siga

Asalin hoton, Getty Images
Bincike ya nuna cewa gurjii na taimakawa wajen rage yawan sukari a jini da kuma hana matsalolin da ke tattare da ciwon siga. Saboda haka, ana bada shawarar gurjii a cikin abincin masu wannan rashin lafiya.
Masaniyar abinci Lilian Felix ta bayyana, "Gurjii na ɗauke da sanadari mai harza mai yawa, wanda ke taimakawa wajen daidaita yawan sukari a jini da hana rage ciwon siga.
Rage ƙiba

Asalin hoton, Getty Images
Gurjii yana da kyau sosai ga waɗanda suke son kula da nauyin jikinsu ko rage ƙiba. Ba ya ɗauke da sinadarin da ke ƙara kuzari da ake kira da 'calory' da yawa, amma yana da sinadarin harza mai yawa wanda ke rage yawan sukari a jini.
Felix ta kara da cewa, "Mun fi bai wa waɗanda suke son rage ƙiba da su riƙa cin gurji sosai saboda harzar da ke cikinsa na taimakawa wajen cika ciki na dogon lokaci sannan yana tallafa wa wajen narkar da abinci yadda ya kamata."
Ƙara ruwa a jiki
Ruwa muhimmin abu ne ga rayuwa—yana taimakawa wajen zagayawar jini da sinadarai a cikin jiki kuma yana taimakawa wajen narkar da abinci da tallafawa aikin koda, da sanyaya jiki.
Gurjii na ɗauke da ruwa har zuwa kashi 95%, wanda ke ƙarawa jiki ruwa sosai.
"Wasu lokuta mutane ba sa shan ruwa sosai a rana, amma haɗa gurji a cikin abinci na iya taimakawa wajen bai wa jiki ruwan da yake buƙata da kuma tallafa wa lafiya gaba ɗaya," in ji Felix.
Inganta lafiyar ciki
Gurji na da amfani wajen sauƙaƙa matsalolin kumewar ciki, da yake gurji na ɗauke da ruwa da kuma sinadarin harza a cikin shi, yana saka mutumin da ke jin wahalar yin baayan gida ya yi shi a sauƙaƙe.
Sanyaya da ƙawata fata

Asalin hoton, Break up
Gurji ba wai kawai yana amfani ga ciki ba ne— yana gyara jiki da kuma taimakawa fata ta yi kyau sosai.
Rage hawan jini
Sinadarin potassium da ke cikin gurji na taimakawa wajen rage yawan sinadarin sodium a jiki wato gishiri mai yawa, wanda sau da yawa ke haifar da hawan jini.
Haɗa gurji a cikin abinci na iya taimakawa lafiyar zuciya da kuma rage hawan jini.
Gargaɗi na musamman

Asalin hoton, Break up
Ga waɗanda suke da lafiya, masana sun bada shawarar cin gurji guda ɗaya a rana ko haɗa shi a cikin abincin yau da kullum. Amma kuma ba kowa ne ya dace ya ci gurjii ba.
Felix ta gargaɗi cewa, "Mutanen da ke da matsalolin lafiyar ciki, kamar ulcer, ko waɗanda ke da matsalar daskarewar jini, bai kamata su ci gurjii ba sai idan likita ya bada shawara ko ya kula da su."









