Da gaske Trump ya saka baki wajen ɗage wa Balogun dakatarwar jan kati?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Dale Johnson
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Football issues correspondent
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 3
Janye dakatarwar da Fifa ta yi wa ɗan wasan Amurka, Folarin Balogun na ci gaba da ɗaukar hankalin magiya bayan ƙwallon ƙafa.
A ƙa'ida a wasan ƙwallon ƙafa, idan aka kori ɗan wasa da jan kati a Gasar Kofin Duniya, to ba zai buga wasa na gaba ba.
Ba wata gardama, ba wata hujja, kuma ba wata damar ɗaukaka ƙara.
Amma matakin da aka ɗauka na soke jan katin da aka nuna wa ɗan gaba na Amurka, ya haifar da tambayoyi da dama da har yanzu ba a samu amsarsu ba.
Balogun - wanda aka kora a wasan da Amurka ta doke Bosnia-Herzegovina a zagayen wasan ƴan 32 - yanzu zai buga karawar da ƙasarsa za ta yi da Belgium ranar Litinin.
Shi ne kan gaba wajen cin ƙwallaye a tawagar Amurka a wannan gasa, inda ya zura ƙwallaye uku
Idan aka yi la'akari da alaƙar da ke tsakanin Fadar White House da Hukumar Kwallon Ƙafa ta Duniya (Fifa), tabbas za a yi tambayoyi kan wannan mataki, kasancewar wani abu ne da ba kasafai ake gani ba wanda ya zo da amfani ga ɗaya daga cikin ƙasashen da ke karɓar baƙuncin gasar.
Kafar yaɗa labaran CBS mai hulda da BBC a Amurka, ya tabbatar da cewa an soke dakatarwar da aka yi wa Balogun ne bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya tattauna ta wayar tarho da shugaban Fifa Gianni Infantino ranar Alhamis game da batun dakatarwar.
Majiyoyin da suka san abin da ya gudana a kiran sun tabbatar wa CBS News hakan.
Shin wannan mataki zai kuma kafa wani sabon tarihi ko sabuwar al'ada a fagen ƙwallon ƙafa?
Me ya sa aka sassauta wa Balogun hukuncin da aka yanke masa, alhali sauran 'yan wasa 11 da aka kora a wannan Gasar Kofin Duniya duk hukuncin dakatarwar ya yi aiki a kansu?
Shin wannan mataki zai sa a riƙa ƙara yawan ɗaukaka ƙara a harkar ƙwallon ƙafa domin rage hukuncin dakatarwa, har ma a lokutan da jan katin ya yi daidai da dokokin wasa?
Idan aka sake korar wani ɗan wasa da jan kati a wannan Gasar Kofin Duniya, kuma aka bayyana a yayin ɗaukar wasan kai tsaye a talabijin cewa "zai rasa wasa na gaba", ya kamata har yanzu a ɗauki hakan a matsayin tabbataccen abu?
A nan, za mu yi nazari kan wannan hukunci, abin da muka sani game da shi, da kuma irin tasirin da zai iya haifarwa a gaba.
Da me Fifa ta dokara wajen matakin?

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Dokokin Gasar Kofin Duniya ba su bai wa tawagogi damar ɗaukaka ƙara kan hukuncin jan kati ba.
Cikin sanarwar da ta fitar game da ɗage hukuncin Balogun, Fifa ba ta bayar da hujja kan matakin nata ba, kawai dai ta ambata sashe na 27 na dokokin ladabtarwarta.
Sashen na 27 yana magana ne kan bai wa Fifa damar ''Dakatar da aiwatar da hukuncin ladabtarwa''.
Sashe ne da ya bai wa fifa damar ɗaukar kowane irin mataki take so ba tare da cikaa wata ƙa'ida ba.
Ba a taɓa amfani da sashen ba tarihin gasar Kofin Duniya.
Haka kuma dakatarwar da aka yi wa Balogun ta wasa ɗaya ce, ba biyu ba, akmar yadda dokokin ladabtarwar suka nuna. Kuma a wannan ma ba a yi bayani ba.
Sashen wasanni na BBC ya nemi sanin yadda hakan ta kasance.
Amma ba ta samu cikakken bayanin dalilin ba. An dai nusar da sashen wasannin na BBC kan haramcin da aka yi wa Cristiano Ronaldo a wasannin neman gurbi kafin fara wannan gasar.
A ƙarƙashin dokokin Fifa, ya kamata a haramta wa Ronaldo wasa uku saboda laifin da ya yi a wasan Portugal da Ireland a wantan Nuwamban bara.
Kan haka ne bai buga wasan ƙarshe na neman gurbi d Armenia, amma kuma sai aka ɗage masa dakatarwar sauran wasannin biyu.
Jan katin Ronaldo da aka ba shi a wasannin neman gurbi, wasu an ganin ba zai yi aiki a gasar ba.
Da gaske Trump ya yi tasiri a matakin?

Asalin hoton, Getty Images
Rahoton CBS ya nuna cewa Shugaban Donald Trump ya kira shugaban Fifa, Gionni Infantino kan batun, inda bayanai suka ce sun tattauna kan matakin.
Bayan tattaunawar tasu ne kuma Fifa ta fito ta sanar da matakin ɗage dakatarwar da ta yi wa Balogun ɗin, wani abu da ya haifar da maganganu daban-daban.
Bayan ta Fifa ta sanar da matakin ne kuma, fadar gwamnatin Amurka ta fiytar da wata sanarwar godiya ga hukumatr ta fifa bisa matakin da ta ɗaukar.
Hukumar ƙwallon ƙafar ta duniya dai ta haramta katsalandan ɗin siyasa a cikin sabgogin ƙwallon ƙafa.
To amma da wannan abu da ya faru, yanzu an fara aza ayar tambaya game da sahihancin matsayin da fifa ke dauka game da siyasa.











