Yadda rayuwar mata take a Iran kafin juyin-juya halin Musulunci

Asalin hoton, Paolo KOCH/Gamma-Rapho vía Getty Images
“Na ga hotuna da dama na kakata kafin juyin juya halin, tana sanye da ɗan kwali na Musulunci, ita kuma mahaifiyata sanye da ɗan siket, suna zaune cikin walwala, tare da juna.
Wannan shi ne abin da Rana Rahimpour, mutumiyar Iran da ke gabatar da shirye-shirye a sashen Fasha na BBC take tunawa, kuma lamarin ba ya danganci iyalanta kawai ba ne.
A Iran, kafin Juyin Juya Hali na Musulunci na shekarar 1979, babu wata doka mai tsauri kamar ta yanzun, da take buƙatar mata, su rufe gashin kansu da shiga irin ta Musulunci.
“Iran ƙasa ce mai sassaucin ra'ayi. Ana ƙyale mata su yi shiga kowacce iri suke so,” in ji ta.
Tana wannan bayani ne a daidai lokacin da ake ta bore da zanga-zanga a gwamman biranen Iran a kan mutuwar wata matashiya mai shekara 22 da jami'an Hisbah na Iran suka kama ta, waɗanda ke tabbatar da an bi dokokin sanya sutura irin ta Musulunci.
An haifi Rahimpour ne bayan juyin juya halin,
Sai dai rayuwar da iyayenta da danginta suka gudanar, da kuma aikinta na jarida, sun bari ta dilmiya ga sauye-sauyen da }asarta ta fuskanta bayan fa]uwar Shah.
Sauyi ne da a farko-farkon shekaru, ya wuce batun sanya tufafi, kamar yadda ƴar jarida ta Iran Feranak Amidi, wacce wakiliya ce a sashen al'amuran mata na BBC, ita ma ta bayyana.
"A da kafin juyin juya hali babu wata wariya ga jinsin mata. Amma bayan shekarar 1979, an ware makarantu, sannan idan aka ga mace da namiji da ba muharraman juna ba suna hulɗa da juna, sai a kama su.”
“A lokacin da nake ƴar shekara goma sha a Iran, ƴan Hisbas sun taɓa kama ni saboda na shiga wani gidan sayar da abinci da wasu abokai.”
“Kafin shekarar 1979, akwai kulab-kulab da ake kwana ana kaɗe-kade da raye-raye da sauran wurare na shaƙatawa da watayawa, da mutane suke da ƴancin cuɗanya da juna yadda suke so.”
Fina-finan da ake kallo kafin juyin juya halin su ma wata shaida ce, na lokacin da mata suke iya zaɓar sanya tufafi irin na Yammacin Turai ko irin na masu ra'ayin riƙau.
“Za ka ga ɗinke-ɗinke na kaya iri-iri. Wasu sukan sa baƙin gyale ko makamancinsa, sai dai ba kamar yadda gwamnati a yanzun ta buƙaci sai an yi ba.”
Zuri'ar Sarakuna
Kafin juyin juya hali na 1979, zuri'ar gidan sarauta na Pahlavi ke mulkin Iran, wacce ta ɗare kan mulki bayan wani juyin mulki.

Asalin hoton, Paolo KOCH/Gamma-Rapho vía Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A shekarar 1926, jagoran juyin mulkin Reza Khan, da aka yi wa sarautar Reza Shah Pahlavi, aka ayyana ɗansa Mohammed Reza Pahlavi a matsayin yarima. Daga bisani, shi ne zai zama Shah na ƙarshe.
A wata maƙala a shekarar 1997, wata cibiyar ƙwararru ta Wilson, ta sake fitar da wata hira da ta yi daga shirinta na tattaunawa a rediyo da Haleh Esfandiary, marubuciyar wani littafi Reconstructed Lives:Women and Islamic Revolution.
Littafin na magana ne a kan sabon tsarin rayuwa da halin da mata suke ciki a juyin juya hali na Musulunci na Iran.
Esfandi ta bar Iran a 1978, sannan ta koma bayan shekara 14 domin gudanar da bincike a kan tasirin juyin juya halin a kan mata.
A wannan hirar, ƴar jaridar ta ce “gwagwarmayar mata a Iran ta soma ne a ƙarshen ƙarni na 19, lokacin da mata suka bazama tituna a lokacin juyin juya hali na tsarin mulki.”
Bayan wannan, sai yawancinsu suka soma gudanar da ayyuka na zamantakewa kamar buɗe makarantu na mata da wallafa mujallu na mata.
Wannan aiki ya soma ne a babban birnin Tehran, sannan ya yi ƙoƙarin yaduwa zuwa sauran lardunan, sannan wannan ya sa “aka samu kafuwar ƙungiyoyin kare haƙƙi na mata.”
Tsarin Musulunci na sa dankwali da hijabi
Sutura ta mata ta rigaya ta zama batu mai muhimmanci a ajandar shugabancin ƙasar a farkon ƙarni na 20.
“Ba a soke ɗaura ]ankwali a hukumance a Iran ba, sai a 1936, a zamanin Reza Shah Pahlavi, uban sabuwar Iran,” in ji marubuciyar.

Asalin hoton, Paolo KOCH/Gamma-Rapho vía Getty Images)
A shekarun farko, shugaban ya ƙarfafa wa mata gwiwar ka da su lulluɓe kawunansu irin na Musulunci a bainar jama'a ko “su ɗaura ɗan kwali maimakon doguwar jallabiya ta gargajiya da suka saba sakawa.”
“Da a ƙarshe aka soke lulluɓe kai a hukumance, tabbas wata nasara ce ga mata, kuma abin tausayi, saboda an raba su da ƴancin zaɓar abin da suke so, kamar yadda yake a lokacin Jumhuriyar Musulunci da aka sake ɓullo da ɗan kwali a shekarar 1979.”
Mata da dama “an tilasta musu yin watsi da gyale, suna fita tituna cikin jin an tursasa musu da kuma tsiraita su”.
Duk da haka, Esfandiari ta nuna cewa uban shah na ƙarshe ya gudanar da wasu sauye-sauye da suka yi tasiri mai kyau a kan mata.
Farin Juyin Juya Hali
A shekarar 1941, ɗan, Mohammed Rexa, ya hau karagar mulki.
A lokacin mulkinsa, “aka soma zamanantar da ƙasar”, kamar yadda Amidi ta bayyana.

Asalin hoton, Getty Images
Wannan matakin ne aka sani da Farin Juyin Juya Hali kuma ya bai wa mata ikon kaɗa ƙuri'a a 1963 da ƴancin siyasa kamar yadda maza suke da shi.
Bugu da ƙari, an yi ƙoƙari wajen inganta kai wa ga samun ilimi a lardunan da ke can gefen gari.
A zamaninsa, aka amince da wata doka ta kariya ga iyali da ta shafi ɓangarori daban-daban, ciki har da aure da saki.
Dokar kamar yadda Amidi ta yi bayani, ta faɗaɗa ƴanci da haƙƙoƙin mata.
“Dokar Ta Kariya Ga Iyali, ta ƙara yawan shekarun da budurwa za ta iya kaiwa, daga 13 zuwa 18 kafin a mata aure, har ila yau ta bai wa mata ƙarin ikon neman miji ya saketa.”
Har ila yau dokar ta taƙaita wa maza auren mace ɗaya kawai.
“Wannan ci gaba ne kam, idan aka kwatanta da sauran ƙasashe da suke yankin.”
Ko da yake Shah, shugaba ne mai ƙarfin iko, shugaba ne mai tafiya da zamani, kuma yake son al'adun Yammacin Turai, saboda haka ya samar da tsari wanda ba ya ba da fifiko ga addini.
Rayuwar yau da kullum
Mata sun fito suna riƙe muƙamai da hawa madafun iko. “Muna da mata ministoci, da alƙalai,” kamar yadda Rahimpour take iya tunawa.

Asalin hoton, Alain MINGAM/Gamma-Rapho via Getty Images
Amma duk da alƙawuran da Farin Juyin Juya Hali ya ɗauka, “an ci gaba da keɓanta mata ga abubuwan da suka saba gudanarwa na al'ada,” in ji Amidi.
Kuma ko da yake ta bayyana cewa “akwai mata a majalisar dokoki”, ta ɗauki mata a matsayin “waɗanda ba sa shiga harkokin siyasa sosai”.
“Sai dai ya kamata mu sa a cikin zuciyarmu cewa kusan rabin shekarun ƙarnin da ya gabata, muta da ke faɗin duniya a wancan lokacin, ba su da iko na siyasa sosai.
Duk da haka, ta nuna cewa mata ƴan uwanta sun soma ƙara ci gaba da taka rawa a rayuwa ta bainar jama'a: “Ana ganin gagarumar tasirinsu a cikin al'umma.
Damuwar mata
Amidi ta nuna “gagarumin tasirin” da Sarauniya Farah Pahlavi, uwar gidan Mohammed Reza, ta samu a kan fasaha da al'adu.

Asalin hoton, Ilya S. Savenok/Getty Images
Tabbas, ayyuka na fasaha sun bunƙasa a Iran a farkon shekarun 1950 da ci gaba zuwa shekarun 1960 da 1970, shi ne batu na rubutun insha'i na Maryam Ekhtiar da Julia Rooney, ta sashen Fasaha ta Islama, da ke Gidan Adana Kayan Tarihi na Fasaha da ke New York.
“A waɗannan shekaru ne aka buɗe Iran ga fagen fasaha na duniya,” kamar yadda aka bayyana.
Yawancin wannan bunƙasar waɗannan aikace-aikace na fasaha, sun girma ne saboda bunƙasar tattalin arziki da ƙasar take samu.
Amma ko da yake Iran tana da ɗumbin man fetur, yawancin ƴan ƙasar ta Iran ba sa amfana da wannan dukiya.
Duk da goyon baya da Shah da uwargidarsa suke ba ayyukan fasaha, masu ayyukan na fasaha, ba a makance suke ga wannan zahiri ba.
Hakazalika ba a makance suke ga tursasawar da gwamnati take yi wa masu adawa da ita ba.
Nahid Hagigat, marubutan sun yi nuni da, “na ɗaya daga cikin ƙalilan na masu ayyukan fasaha da suka nuna damuwar mata a shekarun da suka gabata, kafin juyin juya halin”.
Taimakekeniya
A shekarar 1971, Mohammed Reza, da ya ayyana kansa a matsayin "Shahanshah” ko “Sarkin Sarakuna”, bai tsaya ga zama ɗaya daga cikin mutane mafi arziki a duniya kawai ba, har ila yau shi jagoranci Iran ne a mai cikakken ikon yin yadda ya ga dama.
Mulkinsa ya ci gaba da murƙushe ƴan siyasa masu sukar lamirin gwamnati.

Asalin hoton, Wally McNamee/Corbis/Getty Images
“A gwamnatin baya (kafin juyin juya hali) mutane suna da ƴanci na zamantakewa, sai dai ba su da ƴanci na siyasa, “ Kamar yadda Rahimpour ta bayyana.
“Waccar babbar matsala ce. Sarki ne yake juya jam'iyyun (siyasa) – al'umma ce wacce ake sa ido a kanta.
"Babu ƴancin ƴan jarida, kuma dukkan wani nau'i na gwagwarmaya ta siyasa, tana iya jefa mutum gidan yari.”
Waɗanda ba su gamsu da irin wannan zama ba, sun bazama tituna, sannan a 1978 an gudanar da manya-manyan zanga-zangar ƙin amincewa da mulkin Shah.
Kamar yadda Esfandiari ta bayyana, nasarar da mata suka samu a zamaninsa, a wuraren ƙarshe an yi watsi da ita.
“Domin mayar da martani ga ƙaruwar ƙorafe-ƙorafe na ƴan gargajiya da al'ada da ke cikin al'umma, Shah ya yi matuƙar rage shigar mata madafun iko.”
Ƴan ƙasar Iran da dama da “addinin bai zama wajibi a gare su ba” su ne suka ba da goyon baya ga Juyin Juya Halin na Islama, kamar yadda Rahimpour ta bayyana. Da dama suna kiran “dimukra]iyya ta gaskiya” suke so.
“Juyin ya samu goyon bayan dukkan ƙungiyoyi: masu sassaucin ra'ayi, da ƴan gurguzu da masu ra'ayin addini.”
Mata, ba tare da tunanin me suke so su sanya ko ƙarfin imaninsu na addini ba, suna cikin guguwar da ta yi sanadiyyar fa]uwar Shah a 1979.
“A macin da ya yi sanadiyyar juyin juya hali, akwai mata ƙwararru ba ɗan kwali, da mata masu tsattsauran ra'ayi sanye da baƙin ɗan kwali da suka saɓa sawa na al'ada; akwai mata daga iyalai masu matsakaicin ƙarfi, daga iyalai marasa ƙarfi tare da ƴaƴansu.
Dukkan waɗannan mata suna tafiya kafaɗa da kafaɗa da juna, da fatan juyin juya halin zai kawo musu ci gaba a matsayinsu na tattalin arziki, da kyautata matsayinsu na zamantakewa.
Sannan uwa uba, ya kyautata matsayinsu a idon doka,”
Kamar yadda Esfandiary ke iya tunawa.
Bambancin alƙibla
Amidi ba ta yi imanin cewa mata “suna jin suna da `yanci” ba, kafin Juyin Juya Halin na Musulunci.

Asalin hoton, ABEDIN TAHERKENAREH/EPA-EFE/REX/Shutterstock
“Har lokacin Iran al'umma ce mai addini da take da matuƙar tsattsauran ra'ayi.
Sai dai idan an waiwayi lokacin, za a ga cewa akwai burin ruguza wannan al'ada da ra'ayin riƙau, don barin mata su su yi fice, da ƙara mamaye gurabe a cikin al'umma.”
Sai dai wannan fice, ta yi ƙarin hasken cewa ba ta yi cikakken tasirin zuwa da kuma ba da baya ba.
Kamar tadda Rahinpour ta faɗa, akwai ra'ayoyi da suke cin karo da juna a kan ko mata suna jin suna da ƙarin ƴancin kai, da ƙarfafa su kafin Juyin Juya Hali na Musulunci.
“Mata masu ra'ayin addini za su ce hankalinsu ya fi kwanciya bayan juyin juya halin, sai dai amma mata masu sassaucin ra`ayi ba za su amince da ra'ayinsu ba.
“Bai kamata ka manta cewa akwai wani sashe na al'umar Iran da ke matuƙar riƙo da addini ba.”
Kuma tabbas akwai wasu matan da suka amince da matakan tsarin.
Ganin hotunan da suke tsibe wajen ajiye kayan tarihi na mata a Iran suna sanye da kayan turawa, ba su rufe kansu ba, wata mata ƴar ƙasar Iran ta nuna mun cewa waɗannan hotuna, ba suna wakiltar gaba]ayan rayuwar mata ba ne, kafin juyin juya halin.
Mata da dama, masu shekaru daban-daban, sun zaɓi sanya hijabi ko ɗan kwali saboda “al'umma ta fi karkata ga tsattsauraun, fiye da zama mai addini idan aka kwatanta da yau.
Bore
Ƴan Iran da dama sun shiga juyin juya halin ne da fatan samun ƴnci, sai dai Rahimpour ta ce nan da nan fatar da suke da ita ta wargaje.

Asalin hoton, Paolo KOCH/Gamma-Rapho vía Getty Images
“Bayan juyin juya halin, mun gane cewa mutane masu ra'ayin addini, da damansu ba sa son sanya ƙananan siket, kuma ga ƴancin da maza da mata suke da shi, shi ya sa har ila yau suka amince da juyin.”
Sai dai, ta ce mutane da dama da suke da ra'ayi “mai zurfi na addini” a Iran, suna da tunanin rufe kai “abu ne na zaɓi.”
“Ya tashi daga zama addini idan aka tilasta.”
Iran tana fama da ɓarkewar bore ko zanga-zanga a sassan ƙasar, bayan mutuwar wata ƴar shekara 22, a lokacin da take tsare a hannun ƴan sanda, saboda zargin ba ta kiyaye da dokokin sanya hijabi ba.
Hukumomi sun ce Mahsa Amini ta riga mu gidan gaskiya ne, sakamakon wasu cututtuka da take fama da su.
Sai dai iyalanta da Iraniyawa masu yawan gaske, sun yi imanin cewa ta rasu ne sakamakon dukan da aka mata.
Da alama zanga-zangar tana nuna shi ne ƙalubale mafi girma da shugabannin Iran suka ta~a fuskanta a ƴan shekarun nan.
Kuma an buɗe sabon babi na boren da ya yi suna a Iran.











