Abubuwan da za su faru daga yanzu zuwa ranar binne Sarauniya Elizabeth

Asalin hoton, Getty Images
Yayin makokin da za a yi a kasa baki daya, za a bai wa mutane damar yin gaisuwar girmamawa ga gawar Sarauniyar, lokacin da za a mika ta Edinburgh sannan a karasa da ita Birnin Landan.
Sarki Charles na III zai yi rangadi zuwa yankuna hudu da suka hada Birtaniya.
Ga jerin wasu abubuwa da za su faru a kowacce rana.
Lahadi 11 ga watan Satumba
Za a dauki akwatin gawar Sarauniya wanda ke ajiye a Balmoral a motar daukar gawa.
Za a dauki gawar a mota daga Balmoral da karfe 10:00 na safe zuwa Edinburgh cikin wata tafiyar kan titi ta awa shida da za a yi ta a hankali, mai nisan kilomita 160.
Akwatin gawar zai isa Fadar Holyroodhouse – inda nan ne mazaunin sarakunan Birtaniya a babban birnin Scottland – a ajiye ta a kan gadon sarauta.
A Landan, Sarki zai je ya hadu da Sakatare Janar na kungiyar kasashen rainon Ingila a Fadar Buckingham.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Litinin 12 ga watan Satumba
Sarki Charles III zai fara zuwa dakin taro na Westminster, inda duka ƴan majalisar ƙasar za su taru domin yi masa ta’aziyya.
Mai dakin Sarki, Camilla ce za ta raka shi, Sarkin zai tafi Edinburgh ta jirgin sama. Wata tafiya da zai yi zuwa yankuna hudu na kasar domin karbar ta’aziyya a matsayinsa na Sarkin Birtaniya.
Da yamma kuma, za a tafi da gawar zuwa Cocin St Gile tare da rakiyar Sarki da mambobin gidan sarauta.
Za a kwantar da gawar ta huta a St Gile na tsawon awa 24 kuma mutane su yi bankwana da ita.
Sannan Sarki zai koma Holyrood, inda zai yi bayani tare da Ministar Scottland, Nicola Sturgeon.
Sannan shi da mai dakinsa su je majalisar Scottland inda nan ma za su karbi ta’aziyya.
Sarki Charles zai raba dare da sauran iyalan gidan sarauta domin yin addu’ar dare a Cocin St Gile.
Talata 13 Satumba
Sarkin zai ci gaba da tafiyarsa zuwa sauran yankunan, inda zai ziyarci Belfast a yankin Arewacin Ireland, tare da rakiyar Camilla.
Za kuma su je Hillsborough Castle domin nuna tsohuwar dangantakar da ke tsakanin Sarauniya da Arewacin Ireland.
Daga nan Sarki zai ga Sakataren yankin Arewacin Ireland, Chris Heaton-Harrris tare da wasu shugabannin jam’iyya. Sannan kakakin majalisar ya zo ya yi gaisuwa a madadin kowa.
Bayan ganawa da shugabannin addinin, Sarki Charles da Camilla za su yi addu’a a Cocin St Anne sannan su koma Landan.
Daga Scotland za a dauki akwatin gawar zuwa filin jirgin sama na Edinburgh zuwa RAF Northolt inda za a tafi da Gimbiya Anne.
Ana sa ran jirgin zai isa Landan bayan karfe 7 na yamma.
Daga nan za a kai ta Fadar Buckingham, inda nan ne gidan sarakunan da ke Landan tun 1837.
End of Wasu labaran da za ku so ku karanta
Laraba 14 Satumba
Za a fitar da gawar daga Fadar Buckingham zuwa dakin taro na Westminster.
Mambobin gidan Sarautar ne za su raka gawar tare da faretin sojoji.
Za a bai wa mutane damar ganin yadda za a fitar da gawar saboda za a bi da ita ta kan titunan Birnin Landan. Za kuma a haska yadda lamuran ke tafiya kai tsaye a gidan talabijin.
Da an kai gawar dakin taro na Westminster za a ajiye ta ta huta a kan gadon da ake ajiye gawa a coci.
Ta ko wacce fuska za a sanya masu gadin wannan gado kuma sojojin da suke yi wa masarautar hidima ne.
Za a yi wata addu’a mara tsayi sannan a bar mutane su shiga.
Alhamis 15 ga Satumba
Tsakanin karfe 2 zuwa 5 na yamma za a yi atisayen yadda za a tafi da ita daga sabuwar Fada zuwa Westminster Abbey, sannan a tafi Wellington Arch.
Ranar za ta zama cikakken kwana na hudu da gawar Sarauniya ke zaune a dakin taro na Westminster.
Dubban masu makoki za a bai wa damar shiga, wajen mafi dadewa a Fadar Westminsterkuma zuciyar gwamnatin Birtaniya.
Ana sa ran Sarki Charles III zai ziyarci Wales.
Litinin 19 Satumba
Za a yi jana’izar kasa baki daya ga Sarauniya a wannan rana a Westminster Abbey da karfe 11:00 na safe.
Za a gayyaci manyan shugabannin duniya zuwa wannan wuri su kasance tare da iyalan Masarautar domin tunawa da rayuwar Sarauniya da kuma ayyukan da ta yi wa al’umma.
Manyan ‘yan siyasar Birtaniya da tsofaffin firaiministocin kasar za su halarci wurin, kuma za a haska taron kai tsaye a gidajen talabijin.
Bayan nan, sai a yi jana’izar, sannan a binne ta a Windsor Castle.
Ranar za ta zama ta hutu, sannan akwai ayyukan da ba za a yi ba, kuma wasu harkokin kasuwancin ma ba za a bude su ba.











