Tottenham na son Savinho, Ƙungiyoyi na rububin Rodrygo

Savinho

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Ɗan wasa Savinho daga Manchester City ya kasance wanda Tottenham ke so ido rufe, yayinda kocinsu Thomas Frank ya dage don ganin lallai ya saye matashin mai shekara 21 daga Brazil, musamman ganin sun yi rashin nasarar daidaitawa kan Eberechi Eze mai shekara 27, da ya je Arsenal. (Independent)

Tottenham ta gabatar da tayi kan ɗan wasan Manchester City, kuma ta ce za ta biya fam miliyan 60.7 don ganin ta mallake Savinho, wanda ke burin komawa Landan. (Talksport)

A kokarin ganin ta ɗauko sabbin 'yanwasa biyu, Tottenham ta amince da yarjejeniyar fam miliyan 43 kan ɗan wasan Como da Argentina, Nico Paz mai shekara 20, amma ƙungiyarsa ta Italiya na neman fam miiyan 60.(Sky Sports Italia - in Italian)

Manchester City da Arsenal da Liverpool na son ɗan wasan Real Madrid da Brazil, Rodrygo mai shekara 24, amma ƙungiyarsa ta Sifaniya ba ta karɓi tayi daga kowa ba tukkunan. (Marca - in Spanish)

Ɗan wasan tsakiya a West Ham da Brazil, Lucas Paqueta mai shekara 27, ya kasance wanda Tottenham da Aston Villa ke farauta. (Daily Mail)

Monaco za ta amince da tayin fam miliyan 47.5 kan ɗan wasan tsakiyar Faransa mai shekara 23, Maghnes Akliouche wanda shi ma Tottenham ke zawarci. (Football Insider)

Mai tsaron raga a Paris St-Germain, Gianluigi Donnarumma ya amince da sharuɗan tafiya Manchester City. (Fabrizio Romano)

Newcastle na shirin karɓan tayi daga Liverpool kan ɗan wasanta na Sweden Alexander Isak mai shekara 25, bayan fafatawarsu a ranar Litinni. (The I paper - subscription required)

Mai tsaron raga a Belgian, Senne Lammens bai haska ba a fafatawar Royal Antwerp' na ranar Lahadi saboda neman tafiya Manchester United kan fam miliyan 17. (Guardian)

Kocin West Ham, Graham Potter ya dawo, sai dai ana bukatar ya zage damtse muddin yana son ya cigaba da zama a wannan mukami. (Mirror)

Chelsea za ta matsa kaimi kan saye ɗan wasan Manchester United da Argentina, Alejandro Garnacho mai shekara 21, da kuma na RB Leipzig Xavi Simons mai shekara 22, idan ta iya rabuwa da 'yan wasa biyu. (Sky Sports)

Leeds na tattauna yarjejeniyar ɗauko ɗan wasan Belgium mai shekara 24, Largie Ramazani domin komawa Valencia kan aro. (Athletic - subscription required)

Arsenal ta amince da yarjejeniya saye ɗan wasan Ireland mai shekara 16, Victor Ozhianvuna daga Shamrock Rovers. (Daily Mail)