Tawagar ƙwallon Australia za ta bai wa Falasɗinawa gudummawa

An wallafa

Australia za ta bayar da wani ɓangare na kuɗin wasan da za ta yi da Falasɗinawa a gurbin neman shiga gasar cin kofin duniya don ayyukan jin kai a Gaza.

Hukumar ƙawallon ƙafa ta Australia ta ce za ta ba da kwatankwacin abin da tawagar Socceroos ɗin za ta bayar.

Kocin Australia Graham Arnold ya ce shirye-shiryen wasan na ranar Talata ya kasance "mai matukar damuwa" dangane da rikicin Isra'ila da Gaza.

An shirya gudanar da wasan ne a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan amma jami'ai sun sauya wurin zuwa Kuwait.

Sama da mutane 1,200 ne aka kashe a jerin hare-haren da ƙungiyar Hamas ta ƙaddamar a Isra'ila tare da yin garkuwa da mutane kusan 240, yayin da hukumomin kiwon lafiya na Gaza suka ce an kashe fiye da 11,000 a yankin.

Falasɗinawa sun buga wasansu na farko tun farkon rikicin ranar Alhamis, inda suka tashi canjaras 0-0 da Lebanon a Sharjah.