Al Hilal ta Saudiyya ta yi wa Messi tayin albashin da ya fi na kowa a duniya

Lionel Messi

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Amma kuma Inter Miami ta Amurka sa ran janye Messin
An wallafa

Kungiyar Al Hilal ta Saudiyya, ta yi wa Messi tayin biyan sa albashin da ya fi na kowanne ɗan ƙwallo a faɗin duniya. (Mirror)

To amma, ƙungiyar Inter Miami a Amurka na sa ran sayen zakaran ɗan wasan na duniya da kuma Sergio Busquets na Barcelona a kaka mai zuwa. (Sport - in Spanish)

Chelsea ta yi wa ɗan wasanta na tsakiya, Mason Mount farashin fam miliyan 70 duk da cewa ɗan Ingilan yana cikin shekarar ƙarshe ta kwanturaginsa a kulob ɗin. (Athletic)

Shi dai Mount yana sha'awar tafiya Bayern Munich ne, domin ya sake haɗuwa da tsohon kocinsa a Chelsea Thomas Tuchel. (Guardian)

Haka kuma zakarun na Jamus wato Bayern Munich na dab da kammala yarjejeniya da mataimakin kocin Chelsea Anthony Barry, ɗan Ingila. (90min)

Ɗan wasan tsakiya na West Ham Declan Rice, a yanzu ba shi Bayern ke matukar so ba, har ma ƙungiyar ta musanta cewa, ta tattauna da wakilan ɗan ƙwallon a makon jiya. (Sky Sports)

Har yanzu Harry Kane ne, ɗan wasan da Manchester United ta fi son ɗauka, a ƙoƙarinta na sayo ɗan zaƙaƙurin ɗan gaba.

Amma fa tana harin ɗaukar wasu 'yan wasan ciki har da matashin ɗan ƙwallon Ajax kuma ɗan ƙasar Ghana Mohammed Kudus, da ɗan gaban Benfica na ƙasar Portugal Goncalo Ramos, idan ta rasa Kane. (Manchester Evening News)

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Fatan Manchester United na sayen Frenkie de Jong na Holland ka iya samun tagomashi daga zawarcin da Barcelona ke yi wa Ilkay Gundogan na Manchester City. (Mirror)

Wakilin Gundogan ya musanta cewa kyaftin ɗin na Manchester City ya yanke shawara kan makomarsa, yana cewa kofarsa a buɗe take har yanzu ga mai buƙata. (Guardian)

Mai yuwuwa ne West Ham ta rabu da kocinta David Moyes a ƙarshen kakar nan ko da ƙungiyar ta kauce wa faɗuwa daga gasar Firimiya. (90min)

Watakila Leeds United ta yi zawarcin tsohon kocin Crystal Palace, Patrick Vieira da bazara, idan Javi Gracia da aka naɗa don ya gaji Jesse Marsch, ya ƙi tsayawa a kulob ɗin. (TalkSPORT)

Ɗan bayan Manchester City Aymeric Laporte, daga ƙasar Sifaniya shi ne wanda Paris St-Germain ta fi son ɗauka a yanzu. (Football Insider)

Chelsea da Tottenham za su yi gogayya wajen zawarcin ɗan bayan Inter Milan da Italiya Alessandro Bastoni a bazara. (Fichajes)

Matashin ɗan gaban Brighton kuma ɗan Jamhuriyar Ireland, Evan Ferguson mai shekara 18 na son ci gaba da zama a ƙungiyar, duk da sha'awar da ƙungiyoyin Firimiyar Ingila da yawa ke nuna wa a kansa. (Sun)

Ƙungiyoyin Firimiya da dama na rububin ɗaukar ɗan bayan Barcelona, mutumin ƙasar Denmark Andreas Christensen. (ESPN)

Ansu Fati na son ci gaba da zama a Barcelona, duk da yake, ba a sa shi wasanni sosai a ƙungiyar. (AS)

David de Gea, ya ce yana jin daɗin zamansa a Manchester United, yayin da ƙungiyar ke tattaunawa da shi don tsaida magana a kan sabon kwanturagi. (Sky Sports)

Ɗan gaban Leeds United da Sifaniya na iya barin ƙungiyar da bazara, idan sun faɗi daga gasar Firimiya. (Football Insider)

Olivier Giroud, na shirin ƙulla sabuwar yarjejeniya da AC Milan, wadda za ta kai har nan da 2024. (Fabrizio Romano)

An yi wa AC Milan tayin ɗan wasan Guinea Naby Keita, kafin ƙarewar kwanturaginsa a Liverpool da bazara. (Calciomercato)

Jose Mourinho ya ce yana son ci gaba da zama a ƙungiyar har nan da 2024, kamar yadda kwanturaginsa ya tanada.

Ana raɗe-raɗin cewa kocin, ɗan ƙasarPortugal zai bar kulob ɗin don koma wa Paris St-Germain. (Corriere dello Sport)