Chelsea ta amince za ta dauki matashin Aston Villa Chukwuemeka

Carney Chukwuemeka

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Chelsea ta cimma yarjejeniya da Aston Villa, domin daukar matashi Carney Chukwuemeka kan fam miliyan 20.

Dan wasan mai shekara 18, bai yi wa Villa wasannin sada zumunta da ta je Australia ba, bayan da yarjejeniyarsa ya kare a kakar da ta wuce.

Chukwuemeka, wanda ya buga wa tawagar Ingila ta matasa 'yan kasa da shekara 19 da suka lashe kofin nahiyar Turai tamaula a makon jiya, ya yi wasa 12 a Premier League a Villa.

Dan kwallon zai zama na uku da Chelsea ta dauka kan fara kakar tamula ta bana.

An yi ta alakanta Chukwuemeka da cewar Barcelona da AC Milan da Borussia Dortmund duk sun yi kokarin daukar dan kwallon.

Chelsea da Villa duk sun tabbatar da cinikin Chukwuemeka, an kuma bashi izinin zuwa birnin Landon domin a auna koshin lafiyarsa.

Tuni Chelsea ta dauki dan wasan tawagar Ingila, Raheem Sterling daga Manchester City kan fam miliyan 50 da dan kwallon Senegal, Kalidou Koulibaly daga Napoli kan fam miliyan 34.

Kocin Chelsea, Thomas Tuchel na kokarin kara karfin kungiyar, wanda ke sha'awar sayen Marc Cucurella, bayan da Brighton ta kawo karshen ciniki da Manchester City kan sayar mata da dan wasan Sifaniya.