Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Alejandro Garnacho zai yi jinyar makonni
Dan wasan Manchester United, Alejandro Garnacho zai yi jinyar makonni, bayan raunin da ya ji a wasa da Southampton a Old Trafford.
Ranar Lahadi United ta tashi 0-0 da Southampton a gasar Premier League karawar mako na 27.
Mai shekara 18 ya shiga fafatawar saura minti 17 a tashi daga wasan, sai Kyle Walker-Peters ya yi masa ketar da aka fitar da shi a karawar.
Fred ne ya canji Garnacho, wanda ya fita daga fili da kafarsa, amma sai da sanduna ya bar Old Trafford.
United za ta kara da Real Betis a Sifaniya a wasa na biyu zagayen 'yan 16 a Europa League ranar Alhamis.
A makon jiya United ta doke Betis a Old Trafford a wasan farko da cin 4-1 raar 9 ga watan Maris.
Daga nan kungiyar Old Trafford za ta karbi bakuncin Fulham a wasan daf da na kusa da na karshe a FA Cup, sannan a yi hutu a kalandar Fifa.
Tun farko tawagar Argentina ta gayyaci Garnacho, domin ya buga mata wasan sada zumunta, karon farko da zai yi mata wasa, yanzu hakan ba zai yiwu ba.
Walker-Peters ya sha kalaman wariya da na cin zarafi a kafar sada zumunta, sakamakon sanadin raunin da ya ji wa matashin dan kwallon.
United, wadda ta lashe Carabao Cup a bana tana ta uku a teburin Premier League da tazarar maki daya tsakaninta da Tottenham.