Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
FA Cup: Man United za ta kara da ko dai Bristol City ko Nottingham Forest
Manchester United za ta fuskanci ko dai Bristol City ko kuma Nottingham Forest a zagaye na biyar a FA Cup cikin watan Fabrairu.
Kungiyar Old Trafford ta kawo wannan matakin ne, bayan da ta ci Newport County 4-2 ranar Lahadi.
Ita kuwa mai buga gasa mai daraja ta shida a Burtaniya, Maidstone United za ta kara da ko dai Sheffield Wednesday ko kuma Coventry City.
Mai buga National League, wadda ta fitar da mai buga Championship Ipswich Town a Portman Road tana cikin wadanda za su kara a zagaye na biyar din.
Mai rike da kofin, Manchester City za ta fuskanci mai buga Premier League Luton Town yayin da Liverpool za ta karbi bakuncin Watford ko kuma Southampton a Anfield.
Za a buga karawar zagaye na biyar a FA Cup tsakanin kungiyoyin ranar 26 ga watan Fabrairu.
Jadawalin zagaye na biyar a FA Cup.
- Blackburn Rovers da Wrexham ko kuma da Newcastle United
- Chelsea ko Aston Villa da Leeds United ko kuma da Plymouth Argyle
- Bournemouth da Leicester City
- Liverpool da Watford ko kuma da Southampton
- Bristol City ko da Nottingham Forest ko kuma da Manchester United
- Wolverhampton Wanderers da Brighton & Hove Albion
- Sheffield Wednesday da Coventry City ko kuma da Maidstone United
- Luton Town da Manchester City