FA Cup: Man United za ta kara da ko dai Bristol City ko Nottingham Forest

FA Cup

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Manchester United za ta fuskanci ko dai Bristol City ko kuma Nottingham Forest a zagaye na biyar a FA Cup cikin watan Fabrairu.

Kungiyar Old Trafford ta kawo wannan matakin ne, bayan da ta ci Newport County 4-2 ranar Lahadi.

Ita kuwa mai buga gasa mai daraja ta shida a Burtaniya, Maidstone United za ta kara da ko dai Sheffield Wednesday ko kuma Coventry City.

Mai buga National League, wadda ta fitar da mai buga Championship Ipswich Town a Portman Road tana cikin wadanda za su kara a zagaye na biyar din.

Mai rike da kofin, Manchester City za ta fuskanci mai buga Premier League Luton Town yayin da Liverpool za ta karbi bakuncin Watford ko kuma Southampton a Anfield.

Za a buga karawar zagaye na biyar a FA Cup tsakanin kungiyoyin ranar 26 ga watan Fabrairu.

Jadawalin zagaye na biyar a FA Cup.

  • Blackburn Rovers da Wrexham ko kuma da Newcastle United
  • Chelsea ko Aston Villa da Leeds United ko kuma da Plymouth Argyle
  • Bournemouth da Leicester City
  • Liverpool da Watford ko kuma da Southampton
  • Bristol City ko da Nottingham Forest ko kuma da Manchester United
  • Wolverhampton Wanderers da Brighton & Hove Albion
  • Sheffield Wednesday da Coventry City ko kuma da Maidstone United
  • Luton Town da Manchester City