Jackson zai ci gaba da taka leda a Chelsea zuwa 2033

 Nicolas Jackson

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Ƙungiyar Chelsea ta tsawaita yarjejeniyarta da Nicolas Jackson ta kara masa kaka biyu, kenan zai ci gaba da taka leda a Stamford Bridge zuwa 2033.

Ɗan ƙwallon tawagar Senegal zai ci gaba da zama a Chelsea kaka tara kenan, wanda ya koma ƙungiyar kan £32m kan fara kakar bara daga Villarreal.

Jackson ya ci ƙwallo 14 a Premier League a kakar da ta wuce da cin takwas a karawa takwas baya - shi ne ya ci wadda suka tashi 1-1 da Crystal Palace ranar Lahadi a Stamford Bridge a Premier League.

Tun kan fara kakar nan, Chelsea ta tsawaita kwantiragin Cole Palmer da kaka biyu, shima sai a 2033 zai bar Stamford Bridge.

Bayan da aka kammala zagaye na uku a Premier League ranar Lahadi, Chelsea ta ci wasa ɗaya da canjaras ɗaya da rashin nasara ɗaya.

Ranar Asabar 14 ga watan Satumba, Chelsea za ta je gidan Bournemouth a wasan mako na hudu a Premier League.