Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Liverpool za ta ɗaukaka ƙara kan jan katin Jones
Liverpool za ta ɗaukaka ƙara kan jan katin da aka bai wa Curtis Jones ranar Asabar a wasan Premier League da Tottenham ta ci 2-1.
An kori ɗan wasan mai shekara 22 daga fili a minti na 26, bayan ƙetar da ya yi wa Yves Bissouma, bayan da VAR ta tabbatar da aikata laifin.
Tun farko alƙalin wasa Simon Hooper ya ba shi katin gargadi kan ƙetar da ya yi daga baya ya sauya hukuncin zuwa jan kati, bayan da ya je ya ga abin da ya faru a VAR.
Jones na fuskantar hukuncin dakatarwar wasa uku, idan aka tabbatar da laifin da ya aikata.
Idan har hukuncin ya tabbata, Jones ba zai buga wa Liverpool wasan Premier League ba da za ta kara da Brighton da Everton da kuma Nottingham Forest.
Ranar Lahadi Liverpool ta fitar da sanarwa kan hukuncin da VAR ta ɗauka na soke kwallon da Luiz Diaz ya zura bisa dalili cewar ya yi satar gida.
Tuni dai aka dakatar da alƙalan wasa Darren England da Dan Cook wasa biyu, wadanda suka kula da VAR a fafatawa tsakanin Tottenham da Liverpool.
Ƙungiyoyin biyu sun buga wasa mai zafi ranar Asabar a karawar mako na bakwai a babbar gasar tamaula ta Ingila.