Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Messi ya ba da shawarar ɗauko Modric, Arsenal na son Phillips
Arsenal za ta sake komawa kan cinikin an wasan Manchester City da Ingila Kalvin Phillips mai shekara 27 a watan Janairu, domin ta ƙara ƙarfafa tsakiyarta.(Fichajes - in Spanish)
Kashe-kashen kuɗin da Chelsea ke yi zai ci gaba a watan Janairu, saboda ƙungiyar na neman ɗan wasan Napoli ɗan gaban Najeriya Victor Osimhen da ɗan gaban Brentford Ivan Toney mai shekara 27. (Guardian)
Ɗan wasan gefe na Barcelona da Spain Lamine Yamal mai shekara 16 sai tsawaita kwantaraginsa da ƙungiyar na tsawon shekara uku, wadda za ta ƙunshi biyan fan biliyan ɗaya kafin a sake shi. (Fabrizio Romano)
Idanun Newcastle na kan ɗan wasan bayan Crystal Palace da Denmark Jochim Andersen wanda take sa ran ɗauka a watan Janairu.(Football Insider)
Barcelona ta shirya sayar da ɗan wasan Spain na gaba Ansu Fati a kaka mai zuwa, lokacin da ɗan wasan mai shekara 20 zai kammala zaman aron da yake yi a Brighton. (Sport - in Spanish)
Lionel Messi ya shawarci Inter Miami ta ɗauko ɗan wasan Real Madrid da Croatia Luka Modric mai shekara 38. (Cadena Ser - in Spanish, via Mirror)
Liverpool ta cimma yarjejeniyar tsawaita kwantaragi da ɗan wasanta Tren Alexander-Arnold, inda zai riƙa ɗaukar fam 200,000 a mako. (Football Insider)
Tottenham na shirin ɗaukar ɗan wasan bayan Bayern Leverkusen da Burkina Faso Edmond Tapsoba mai shekara 24 nan da watan Janairu mai zuwa. (Fichajes - in Spanish)
Juventus na yunƙurin ƙara shawo kan ɗan wasan Faransa Adrien Rabiot mai shekara 28 domin sake tsawaita kwantaraginsa da shekara uku, bayan ya yi watsi da tayin da Manchester United ta yi masa a farkon kakar nan na zaman shekara ɗaya da yarjejeniyar tsawaitawa. (Tuttosport)