Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Fitattun ƴan ƙwallon Afirka da ke haskawa a nahiyar Turai
Ƙwallon ƙafa ya kasance wasa mafi farin a duniya tsakanin sauran wasanin a ake da su.
An yi fitattun 'yan ƙwallo da duniya ba za ta taɓa mantawa da su ba sakamakon irin bajintar da suka yi wajen kafa tarihi a fagen wasan.
Kuma nahiyar Turai ta kasance nahiyar da wasan ya fi zarra da farin jini kodayake a baya-bayan nan wasan na samun bunƙasa da karɓuwa a sauran nahiyoyin duniya.
To sai duk da shaharar da nahiyar Turai da yi a taka leda ba asalin 'yan wasan nahiyar ba ne kawai tauraruwarsau ke haskawa a fagen ba.
A wannan maƙala mun zaƙulo muku wasu daga cikin fitattun ƴan Afirka waɗanda 'ludayinsu ke kan dawo' a fagen tamaular nahiyar Turai.
Ademola Lookman
Ɗan wasan gaban na Najeriya na ɗaya daga cikin fitattun 'yan Afirka da ke haskawa a nahiyar Turai.
Gwarzon ɗan wasan na Afrika na 2024 ya taimaka wa na ƙungiyarsa ta Atalanta da ke Italiya ta lashe gasar kofin zakarun Turai ta Europa a watan Mayun 2024, bayan da ya zura ƙwallo uku rigis.
Lookman ya kuma taimaka wa Najeriya ta kai wasan ƙarshe na gasar kofin Afirka ta CAF da aka gudanar a ƙasar Ivory Coast a farkon shekarar 2024, inda ya ci ƙwallo uku a gasar.
Ɗan wasan na ɗaya daga cikin 'yan wasan da ke ɗaukar hankali a nahiyar Turai.
Simon Adingra
Ɗan wasan bayan na Ivory Coast na ɗaya daga cikin ginshiƙan ƙungiyar Brighton & Hove Albion da ke buga gasar Premier League ta ƙasar Ingila.
Adingra ya taimaka wa Ivory Coast lashe gasar kofin ƙasashen Afirka ta CAF da ƙasarta ta karɓi baƙunci.
Ya kuma kasance cikin mutane da suka yi takarar lashe kyautar gwarzon ɗan wasan Afirka da ake bai wa ɗan wasan da ya fi ƙwazo a nahiyar.
Mohamed Salah
Ɗan wasan ɗan asalin ƙasar Masar ya kasance jigo a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Liverpool da ke ƙasar Ingila.
Ɗan wasan ya taimaka wa ƙungiyar ta koma kan ganiyarta tun bayan da ya koma Ingila a watan Yunin 2017.
Ya taimaka wa ƙungiyar lashe kofin gasar Premier a 2020, kafin nan ya taimaka mata ta ɗauki kofin zakarun Turai ta Champions League a 2019.
A baya-bayan nan an yi ta alaƙanta ɗan wasan da komawa taka-leda ƙasar Saudiyya, bayan saɓanin da ya samu da tsohon kocin ƙungiyar Jürgen Klopp.
Mohammed Kudus
Ɗan wasan tsakiyar Ghana na daga cikin fitattun 'yan wasan ƙwallon ƙafar Afirka da ke taka leda a nahiyar Turai.
Kudus da ke wasa a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta West Ham a Birtaniya, na daya daga cikin manyan 'yan wasan da kungiyar ke alfahari da su.
Serhou Guirassy
Ɗan wasan ɗan asalin ƙasar Benin na taka leda ne a ƙungiyar Borussia Dortmund mai buga gasar Bundesliga ta ƙasar Jamus.
Ya kasance cikin fitattun 'yan wasa da ƙungiyar ke alfahari da su.
Guirassy na ɗaya daga cikin 'yan wasan da suka yi takarar gwarzon ɗan wasan Afirka na 2024.
Achraf Hakimi
Ɗan wasan ɗan asalin ƙasar Morocco na daga cikin zaƙaƙuran 'yan ƙwallo da ke taka leda a ƙungiyoyin nahiyar Turai
Ya fara fice a lokacin da yake ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid, kafin daga bisani ya koma PSG da ke Faransa.
Ɗan wasan bayan ya taimaka wa ƙungiyar ta PSG lashe kofuna a ƙasar Faransa, sannan ya taimaka wa ƙasarta ta Morocco kai wa matakin wasan kusa da na ƙarshe a gasar cin Kofin Duniya da aka buga a ƙasar Qatar.
Shi ma ya shiga jerin 'yan wasan da suka yi takarar gwarzon ɗan wasan Afirka ta 2024.
Victor Osimhen
Ɗan wasan gaban na Najeriya na ɗaya daga cikin 'yan wasan da ke taka rawar gani a nahiyar Turai.
A shekarar 2023 ya taimaka wa ƙungiyarsa ta Napoli lashe kofin Seria A karon farko cikin shekara 33.
A shekarar ne ɗan wasan ya kasance wanda ya fi kowa cin ƙwallo a gasar, bayan da ya zura ƙwallo 26 a kakar.
Shi ne ɗan wasan Afirka mafi ƙwazo a shekarar 2023.
A yanzu haka ɗan wasan na taka-leda a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Galatasaray S.K. da ke Turkiyya.
Amad Diallo
Ɗan wasan ɗan asalin ƙasar Ivory Coast a baya-bayan nan ya kasance cikin matasan 'yan wasa da ke tashe a nahiyar Turai.
Ɗan wasan da ke taka-leda a ƙungiyar Manchester United ya haska sosai a wasan bayan-bayan nan da ƙungiyarsa ta buga da Manchester City a gasar Premier League bayan da ya zura ƙwallon da ta bai wa ƙungiyarsa nasara a wasan.
Haka nan ana masa kallon matashi wanda tauraruwarsa za ta iya ci gaba da haskawa a harkar tamaula har nan da shekaru masu zuwa.
André Onana
A duk inda ake batun samun nasarar ƙungiya dole ne a jinjina wa mai tsaron raga.
Ɗan wasan mai tsaron ragar ɗan asalin ƙasar Kamaru, na taka leda a ƙungiyar ƙwallon ƙwafa ta Manchester United.
Ya kuma kasance cikin fitattun 'yan Afirka da ke haskakawa a nahiyar Turai.
Thomas Partey
Wani ɗan Ghanan da shi ma ke haskawa a nahiyar Turai shi ne Thomas Partey da ke wasa a ƙungiyar Arsenal.
Thomas Partey, ɗan asalin ƙasar Ghana, ya kasance mai wasa a tsakiyar fili.
Tun bayan kamawar kakar wasanni ta 2024/25, Partey ya taka muhimmiyar rawa a nasarorin da Arsenal ta samu.