Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ƙasarka ta fi kulob ɗinka muhimmanci - Harry Kane
Kyaftin Harry Kane ya nuna ɓacin ransa kan yawan ƴan wasan da suka fice daga tawagar Ingila ta baya-bayan nan, yana mai cewa “Ingila ta fi kowane kulob muhimmanci”.
Ƴan wasa tara sun fice daga cikin tawagar Lee Carsley na wasanni biyu na ƙarshe da zai jagoranta a matsayin kocin riƙon ƙwarya kafin Thomas Tuchel ya karɓi ragamar horas da ƴan wasan a watan Janairu.
Kane ya shaidawa manema labarai cewa "Ina ganin Ingila ta fi lkomai muhimmanci. Ingila ce ke gaban kulob."
"A matsayin ka na ƙwararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa, ƙasarka ita ce abu mafi mahimmanci, kuma lokacin da Gareth [Southgate] ya ke koci ya mai da hankali akan hakan kuma bai ji tsoron yanke hukunci kan kowanne ɗan wasa ba.''
Ingila za ta fafata ta Girka a ranar Alhamis a filin wasan Olympiako Stadio Spyros Louis kafin ta karɓi baƙuncin Jamhurriyar Irelend ranar Lahadi 17 ga wannan watan na Nuwamba duk a gasar Uefa Nations League.
Ingila dai ta samu nasara a wasanni uku cikin huɗu da ta buga a gasar, bayan da ta sha kashi a hannun Girka a wasanta na ƙarshe.