Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Malamin makarantar da hauhawar farashi ta jefa cikin matsanancin talauci
- Marubuci, Umaymah Sani Abdulmumin
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multimedia Broadcast Journalist
- An wallafa
"Ba a shiga tsakiyar wata nake shiga tunanin da laluben hanyar samun abin ciyar da iyalina, wannan yanayi kusan kowani ma’aikacin LEA a inda nake na fama, mun rasa mafita", wadannan su ne kalmomin Ahmed Sani Alangawari malamin makaranta a jihar Bauchin Najeriya.
Ahmed Sani yana da shekara 38 a duniya, kuma matarsa ɗaya da yara uku, sannan a inda yake koyarwa albashinsa naira dubu 41 ne.
Malamin ya ce a kowane lokaci baya cikin kwanciyar hankali la'akari da hauhawan farashi da kuma karancin albashi, shekara da shekaru babu wani sauyi.
Ahmed ya aiko da labarinsa ne a cikin jerin labaran da BBC Hausa take samu daga ƴan ƙasar, bayan wallafa neman jin ra'ayin mutane a wani shirin tattara labarai na musamman gabanin zaɓukan 2023.
A cikin bayyanansa ya yi bayanai dalla-dalla kan yadda ya ke gudanar da rayuwa da naira dubu 41 da yake karɓa a matsayin albashi.
"Rayuwar malami mai cike da akuba"
Malamin mazaunin garin Azare ya ce a karamar hukumar Zaki yake aiki, kuma idan ya kasafta albashinsa, a kullum yana kashe dubu biyar kan abinci da ba wai me gina jiki ba ne.
Sannan kuɗin mota na kai masa naira dubu ɗaya a kullum, kuma rabonsa da karin matsayi a aiki tun 2015.
Ba shi da wata hanyar samun kuɗi, face noma da wasu ayyuka ɗaiɗaiku haka da ke shigo musu, amma ba komai ba.
Ahmed ya ce abin da a baya yake siya naira 500 yanzu ya koma 1,500 don haka kawai Allah ke rufa asiri da shiga lamarinsu.
Malamin ya ce a kullum ana cikin bashi, saboda kuɗin ba sa isarsa har a kai ga ƙarshen wata.
Ya ce ba shi kaɗai ba, kusan a yankin da ya ke aiki kowa kuka yake da talauci, tamkar gwamnati ba ta san da su ba.
Ya ce duk da cewa matsin tattalin arziki ba wai a Najeriya kadai ake fama ba kusan matsala ce ta duniya, kasashen da suka samu cigaba na bijiro da dabarun saukaka rayuwar talakawa.
Amma abin mamaki a Najeriya kusan ba za a ce ga wani tsari ko dabaru da aka bijiro da shi domin saukakawa talaka da sauran 'yan kasa da ke cikin matsi ba.
Akwai bukatar a ce gwamnati tana la'akari da 'yan kasarta wajen wasu tsare-tsare da neman hanyar ceto mutane daga kangin da suke ciki.
End of Karin labaran da za ku so karantawa
"Babu wani sauyi da nake gani"
Na kamala digiri da daraja ta biyu a fannin noma, na kuma yi HND shi ma da daraja ta biyu na kammala, na kuma yi digiri ta biyu, amma abin mamaki ban samu wani aiki mai karfi ba.
Na sha matuƙar wahala, karshenta na samun aikin koyarwa a makarantar firamaren gwamnati da ke karkashin karamar hukuma.
Ga shi kuma wani abin takaici albashi baya zuwa kan lokaci, sai kusan an gama biyan kowanne ma'aikaci gwamnati sannan namu albashi ke zuwa.
Idan mutum ya yi la'akari ga gwagwarmayar rayuwarsa, wajen neman ilimi har zuwa wannan mataki, kusan kawai babu riba.
Sannan Najeriya kasa ce da samun aiki sai ɗan wane da wane, duk kwazonka, indai ba rabo mai karfi ya tsaga da kai ba, hakanan zaka ta zama babu abin kirki ko aikin yi mai karfi.
Najeriya ba ta da tsarin inganta wannan matsala, ko inganta albashin malaman makarantu, shiyasa mu ka fi kowani ma'aikaci talauci, albashin ko abinci kirki baya iya siya mana balanatana kula da iyali.
Na yi tunanin wata rana hakan zai sauya a Najeriya, amma lura da yada abubuwan ke tafiya da wuya muga sauyi nan kusa.
Ban taɓa tunanin da matsayin karatu na zan shiga akuba da wahala ba.
Bai dace a bai wa fannin ilimin firamare a hannun gwamnatin Jihar ba, saboda basa iya gudanar da ita, shiyasa ko 'ya'yansu ma da masu hannu da shuni ba sa zuwa irin makarantun.
Kuma abin da ake mantawa shi ne indai ba a inganta karatun firamare an daina raina aikin ba, to cigaban hakan zata rinka tafiyar hawaniya da fuskantar koma-baya.
"Yan siyasa bukatunsu ne gabansu"
"Kusan ina iya cewa galibin 'yan siyasa bukatunsu ce kawai a gabansu, kullum za ka ji suna maganar inganta ilimi amma idan aka zurfafa bincike kusan babu wani abin a zo a nuna.
"Daidaiku ne kawai ke tabuka abin a zo a gani."
Ahmed ya ce, akwai bukatar sauya abubuwa da dama a wannan kasa, kuma kukan talauci da ake yi muddin ba a inganta fannin ilimin firamare ba, koma baya za a rinƙa gani a kullum
Ahmed ya bada misali da wani abokinsa da ya ce a Kenya yake koyarwa amma albashinsa ya wuce tunani, sannan ga rayuwar rufin asiri.
Malamin ya ce muddin gwamnatoci bata tashi tsaye wajen neman wa malamai da dalibai mafita a rayuwa ba, su ma daga ɓangaresu haka za a cigaba da samun ɓata-gari saboda tsananin talauci.
Ahmed ya ce a yanzu dai yana fafutikar samun kananan ayyuka da kuma kokari a fanin noma, wanda a ganinsa su ne za su iya za me masa mafita nan gaba.
Sannan ya ce duk da cewa yana koyarwa, la'akari da rashin inganci makarantu firamare saboda rashawa a wanan fannin, yaransu biyu makaranta kudi ya kai su, da ko yaushe yake fafutikar ganin ya samu hanyar biya musu kudin makaranta.
"Fatana shi ne gwamnatoci na gaba su saurare kokenmu ko rayuwarmu ko ta yaya za ta inganta anan gaba".