Waiwaye: Ƙarar El-Rufai da sace mahaifiyar Rarara

An wallafa

Wannan maƙala ce da ke kawo maku muhimman abubuwan da suka faru a Najeriya cikin makon da ya gabata.

NCDC ta buɗe cibiyar agajin gaggawa saboda ɓarkewar cutar kwalara a Najeriya

CHOLERA

Asalin hoton, GETTY IMAGES

A cikin makon jiyan ne kuma Hukumar hana yaɗuwar cututtuka a Najeriya NCDC ta buɗe cibiyar bayar da agajin gaggawa yayin da adadin waɗanda suka mutu sakamakon kamuwa da cutar kwalara ya kai 53 a fadin ƙasar.

A cewar sanarwar da hukumar ta NCDC ta fitar a ranar Litinin din da ta gabata kan dandalinta na, wani bincike da aka yi kan hadarin kamuwa da cutar ya nuna akwai matukar hadarin kamuwa da cutar sosai, dalilin da ya saka aka buɗe cibiyar bayar da da agajin gaggawa ta ƙasa EOC.

“Ya zuwa ranar 24 ga Yuni, 2024, an samu jimillar mutane 1,528 da ake zargi da kamuwa da cutar da kuma mutuwar mutum 53 a cikin jihohi 31,” in ji NCDC.

Hukumar ta kuma jaddada buƙatar a kara wayar da kan jama’a da daukar matakan kariya domin dakile yaduwar cutar.

El-Rufa'i ya maka majalisar dokokin Kaduna a kotu

Elrufai

Asalin hoton, Others

A ranar Larabar makon jiya, tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i ya shigar da ƙara a gaban kotu, inda yake ƙalubalantar majalisar dokokin jihar kan zarge-zargen da ta yi masa na almundahana da kuɗin gwamnati a lokacin mulkinsa.

Gwamnan ya shigar da ƙarar ne a ranar Laraba a wata babbar kotun tarayya da ke birnin Kaduna.

Wata sanarwa da tsohon gwamnan ya fitar ta hannun mai ba shi shawara kan yaɗa labaru, Muyiwa Adekeye, ta ce Elrufa'i ya shigar da ƙarar ce domin tabbatar da haƙoƙoƙin da yake da shi na kare kai game da binciken da majalisar dokokin jihar ta ce ta yi a kansa.

Lauyan El-Rufa'i, AU Mustapha ya ce tsohon gwamnan ya ɗauki matakin ne ganin cewa yana da hakkin a saurare shi a duk wani mataki na bincike ko kotu da za a ɗauka kansa, kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada.

Gwamnonin Arewa sun lashi takobin kawo karshen matsalar tsaro a jihohinsu

NGF

Asalin hoton, KATSINA STATE GOVERNMENT

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A cikin makon jiyan dai, Ƙungiyar gwamnonin arewa maso yammacin Najeriya ta kafa wani kwamiti da zai rika tuntubar juna da aiwatar da abubuwan da aka cimma bayan, kammala taron inganta zaman lafiya da tsaro a yankin da aka gudanar a Katsina.

An gudanar da taron ne da hadin gwiwar hukumar raya kasashe ta majalisar dinkin duniya inda ƙwararru da sauran masu ruwa da tsaki a sha’anin tsaro suka yi gagarumar tattaunawa ta kwana biyu tare da cimma matsaya kan abubuwa da dama wadanda za su taimaka wajen magance matsalar tsaron da ke addabar yankin.

Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda shi ne shugaban kungiyar gwamnonin arewa maso yamman, kuma ya shaida wa BBC cewa taron ya sha banban da wadanda aka sha gudanarwa a baya.

Ya ce ganin irin fuskokin da suka halarci taron, hakan ya nuna musu cewar matsalar tsaron da ake fama da ita a yankin ta dami kowa, wanda yasa mutanen da a baya suke yi wa lamarin ruƙon sakainar kashi, yanzu kowa ya fahimci cewar dole ne a haɗa hannu wajen ganin an ɗauki matakai da za su kawo ƙarshen matsalar.

Tinubu ya amince da bayar da tallafin N50,000 ga iyalai 100,000 a kowace jiha har wata uku

Tinubu

Asalin hoton, BOLA TINUBU/X

A ranar Alhamis ɗin makon jiya, shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya amince da matakin bayar da tallafin naira dubu 50 ga iyalai dubu 100,000 a kowace jiha a faɗin ƙasar.

Shugaban ƙasar ya amince da matakin ne bayan tattaunawa da gwamnonin jihohin ƙasar a taron majalisar tattalin arziki ta ƙasa da ya gudana a fadar shugaban ƙasar ranar Alhamis

Shugaba Tinubu ya kuma amince da ware naira biliyan 155 domin sayen kayan abinci da za a raba a jihohin ƙasar domin rage masu raɗaɗi.

Haka kuma taron ya amince da fara aikin babban titin Sokoto zuwa Badagry da zai ratsa jihohin Sokoto da Kebbi da Neja da Kwara da Oyo da Ogun da kuma jihar Legas.

'Ƴan bindiga' sun sace mahaifiyar mawaƙi Dauda Kahutu Rarara

Rarara

Asalin hoton, FB/DAUDA KAHUTU RARARA

A ranar juma'ar makon jiya, rundunar ƴansandan Najeriya a jihar Katsina ta ce ta kama mutum biyu bisa zargin su da hannu a garkuwa da mahaifiyar wani fitaccen mawaƙin Hausa, Dauda Kahutu Rarara.

A tattaunawarsa da BBC, Mai magana da yawun rundunar a Katsina, Sadiq Hikima ya ce "muna tsare da mutum biyu kan lamarin, muna ci gaba da bincike".

Tun farko, kwamishinan tsaro na jihar Katsina, Nasiru Mu'azu ya ce an sace dattijuwar ce a daren Juma'a a ƙauyen Kahutu da ke ƙaramar hukumar Ɗanja.