INEC ta kammala shirin zabe a Osun
INEC ta kammala shirin zaben gwamna a Jihar Osun

Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya wato INEC, ta ce ta kammala shirinta tsaf na gudanar da zaben gwamna da za ayi a jihar Osun da ke kudu maso yammacin kasar.
Hukumar ta ce ta yi hakan ne don gudun samun wasu matsaloli a ranar zaben.
INEC, ta ce yayin da ya rage lokaci kalilan a fara kada kuri’a a fadin jihar, tuni ta rarraba takardun zabe ga kananan hukumomin jihar 30.
A gaban jami’an tsaro aka kammala rarraba kayayyakin zabe masu muhimmanci.
Hajiya Zainab Aminu, jami’a ce a hukumar wadda kuma ta je Osogbo don ganin yadda zaben zai wakana, kuma ta shaida wa BBC cewa hukumar ta yi nasarar rarraba kayayyakin ne da suka hada da takardar kada kuri’a da kuma takardar rubuta sakamakon zabe.
Hajiya Zainab, ta ce sai da hukumar ta INEC, ta fara aikewa da kayan zaben ga kananan hukumomin da ke da nisa saboda su isa da wuri har a samu a rabasu zuwa gundumomi daga nan kuma sai rumfunar zabe.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Jami’ar INEC din ta ce kayan zaben sun isa kananan hukumomin jihar ba tare da wata matsala ba.
A ranar Alhamis ne aka kammala gangamin yakin neman zaben gwamnan da jam’iyyun siyasa 15 za su fafata.
Wakilin BBC da ke babban birnin jihar Osun din Osogbo, ya ce an samar da cikakken tsaro don sanya idanu a kan zaben.
Ya ce tuni rundunar ‘yan sandan Najeriya ta aike da dubban jami’an ‘yan sanda, haka hukumar jami’an tsaro ta farin kaya ma ta aike da nata jami’an zuwa jihar.
Hukumar ta INEC dai ta ce ta gamsu da yanayin tsaron ta ga an samar saboda tunkarar zaben gwamnan da za a yi a ranar Asabar.
Inda Hajiya Zainab, ta ce idan ba bu tsaro zaben ma sai ya samu matsala.
A yanzu haka rahotanni sun ce jam’iyyar PRP, ta sanar da janyewa daga zaben.
Sakataren jam’iyyar na kasa ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar kasa da sa’oi 48 kafin zaben gwamnan ya gudana.
A karshe hukumar zaben ta ce ta yi hakan ne domin tabbatar da an samu nasarar gudanar da zaben gwamna kamar yadda aka tsara yi a ranar Asabar mai zuwa.











