Wasu batutuwa kan wasan da Barca ta doke Real a Amurka

Barca Real

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Barcelona ta yi nasa a wasan hamayya na Clasico na farko a 2024/25, bayan da ta doke Real Madrid 2-1 a filin wasa na MetLife da ke New Jersey a Amurka

Bangarorin biyu sun buga karawar ba tare da manyan taurarunsu ba, waɗanda ke hutu, duk da haka sun buga karawar mai ban sha'awa.

Fitattun ƙungiyoyin Sifaniya na buga wasannin shirye-shiryen tunkarar kaka ba a Amurka, bayan da kowacce ke fatan taka rawar da ta dace.

Daga gani kasan cewar ƴan wasan da Real Madrid ta yi amfani da su a wasa da Barcelona ba sune za su buga Uefa Super Cup ba da Atalanta.

Koda yake wasu fitattun ƴan wasanta suna Amurka, inda take buga atisayen da ya hada da Thibaut Courtois da Antonio Rudiger da Luka Modric da kuma Vinicius Junior.

To amma har yanzu Jude Bellingham da Kylian Mbappe da Federico Valverde da kuma Dani Carvajal, suna hutu bayan da suka buga Euro 2024.

Ƙungiyoyin sun taka rawar gani a fafatawar, inda kowacce ta kai hari 11, koda yake Barcelona ce ta yi nasara a wasan hamayyar da suka yi a Amurka.

Sabon ɗan wasan da Real ta ɗauka a bana, Endrick ya buga wasan tare da Arda Guler da Brahim Diaz, to amma watakila ɗan kasar Brazil ya yi zaman benci a kakar nan.

Hakan zai sa matashin ya kara sanin wasu dabarun tamaula da ake yi a Turai da kara gogewa, kafin daga baya Real ta more shi.

Barcelona na kokarin sayar da wasu 'yan wasanta, domin ta samu damar ɗauko fitattun da za su taka mata rawa a bana, bayan da ta yi ta biyu a La Liga a bara.

Ana ta alakanta ɗan wasan Brazil, Raphinha da cewar zai bar Barcelona kan fara kakar nan, yayin da ake cewa Ilkay Gundogan zai koma Saudi Arabia.

Wasan sada zumunta da Barcelona ke yi a Amurka yana kara mata kwarin gwiwa cewar sabon koci, Hansi Flick zai yi abin kirki a kakar bana.