Abubuwan da suka haddasa tsadar takin zamani a Najeriya

Asalin hoton, Getty Images
Kamfanonin da ke sarrafa takin zamani a Najeriya sun bayyana cewa dalilai da dama ne suka haddasa tsadarsa a wannan shekarar.
Suna bayanin ne a yayin da manoma ke ci gaba da kokawa kan tsadar takin na zamani, lamarin da ya haifar da fargabar cewa zai iya illa ga manoma ta hanyar rage yawan amfanin gona da suke iya samarwa a daminar bana.
Shugaban kungiyar manoma shinkafa ta Najeriya, Abubakar Aliyu Haruna, ya shaida wa BBC tsadar takin za ta shafi noman shinkafa a arewacin Najeriya a wannan daminar.
Ya ce “A bara akan sayi buhun takin zamani a farashin da ya kama daga dubu bakwai zuwa dubu goma, amma a wannan shekarar takin yakan kai har dubu ashirin da shidda ko da biyar.”
Sai dai a martanin da suka mayar, wasu manyan kamfanonin sarrafa takin zamani a kasar sun yi bayani game da dalilan da suka haddasa karanci da kuma tsadar takin zamani a kasar.
Malam Mas’ud Lawal, jami’i a kamfanin sarrafa takin zamani na Barbados da ke Kaduna, ya ce akwai wasu dalilai da suka sanya takin ya yi tsada kamar haka:
Tashin farashin dala
Malam Mas’ud ya ce yawanci kayan da ake bukata domin hada takin zamani ana sayo su ne daga kasashen waje.
Kuma a cewarsa ana amfani ne da dala wajen cinikayyar irin wadannan sanadarai, shi ya sa tashin farashin dala kan sanya kayan su kara tsada.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Tsadar man dizel
Ana amfani ne da manyan motoci wurin safarar kayan da ake bukata wajen hada takin zamani daga bakin ruwa zuwa kamfanoni.
Karanci da kuma tashin farashin litar man dizel din na daya daga cikin manyan dalilan tashin farashin na buhun taki.
A cewarsa baya ga motoci da ke dakon kaya daga bakin teku zuwa kamfanoni, injinan da ke sarrafa takin zamanin su ma suna amfani ne da man na dizel, saboda haka tsadar sa ta sanya kudin takin ya kara tashi.
Raunin tattalin arzikin al'umma
Ya kuma ce karancin kudi da hali na tsadar rayuwa a Najeriyar su ma sun sanya manoma da dama ba su iya sayen takin.
Sauran abubuwan da Malam Lawal ya bayyana a matsayin wadanda suka bayar da gudumawa wajen tashin farashin takin na zamani su ne tsadar kudin lantarki, da kuma yakin da ake yi tsakanin Ukraine da Rasha.
Sai dai a cewar sa duk da haka gwamnatin Najeriya ta yi kokari wajen ganin takin bai yi tsadar da ta wuce misali ba, ta hanyar kayyade farashin wasu nau’ukan takin na zamani da aka fi amfani da su.
Misalin irin wannan taki shi ne NPK 20-10-10 wanda gwamnatin Najeriyar ta ce kada a sayar da shi a farashin da ya wuce Naira dubu ashirin da biyu da dari bakwai.










