Rashford ya koma kan 'ganiya' bayan hutu da ya yi

Asalin hoton, Getty Images
Dan kwallon Manchester United, Marcus Rahford, ya ce ya koma kan ganiya bayan hutu da ya yi, sakamakon kammala kakar da ta wuce.
Ya kuma kara da cewar zuwan sabon koci Erik ten Hag ya zaburar da ’yan wasa, don fuskantar kakar da za a fara a cikin watan Agusta.
United ta samu maki mafi muni a tarihin da take buga Premier League a kakar da ta wuce, inda magoya baya suka zargi Rashford, wanda ya ci kwallo biyar da rashin tagazawa.
Shi kanshi dan wasan ya fuskanci kaka mafi muni da bai sa kwazo ba kamar yadda ya kamata a tarihin buga Premier League da ya ke yi.
Dan kwallon tawagar Ingila ya ce wannan hutun da ya yi ya kara samun kuzari, yana fatan haka sauran abokanan taka ledarsa ke ji.
United za ta buga wasannin atisayen tunkarar kakar da za a fara a bana, inda za ta ziyarci Bangkok da Thailand da Melbourne da Australia da kumaPerth.
Haka kuma kungiyar za ta ziyarci Oslo da Norway, sannan ta karkare da wasan sada zumunta a Old Trafford, domin magoya baya su shaida shirye-shiryen da ta yi.







