Man United na fatan daukar Malacia daga Feyenoord

Tyrell Malacia

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Manchester United na fatan kammala cinikin fam miliyan 13 kudin daukar mai tsaron baya, Tyrell Malacia daga Feyenoord.

Ana cin karo da takaddama a cinikin dan wasan mai shekara 22, daga wakilan kungiyar Malacia.

Wanda yake kula da harkokin dan wasan tawagar Netherlands shi ne dai ke wakiltar Frenkie De Jong, wanda United ke son dauka a bana.

Tun farko Malacia na son wani daga iyalin dan kwallon ya shiga cikin lamarin, amma yanzu an kamo bakin zaren.

Mai tsaron baya daga gefen hagu, wanda ya lashe Dutch Cup biyar, yana cikin 'yan wasan da suka bugawa Feyenoord wasan karshe a Europa Conference League da Roma ta lashe a kakar da ta wuce.

Kungiyar Lyon ta yi zawarcin dan wasan, daga baya United ta shiga cinikin ta yi kane-kane.

United za ta je Bangkok domin yin atisayen tunkarar kaka bana ranar 8 ga watan Yuli, inda za ta kara da Liverpool kwana hudu tsakani.