Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Man Utd za ta dawo da Depay, Chelsea da Madrid na neman Endrick
Manchester United ta tattauna a kan kara sayen tsohon dan wasanta Memphis Depay daga Barcelona, wadda daman watakila ta soke kwantiraginta da dan gaban na Holland.
Chelsea da Real Madrid na ci gaba da zawarcin dan wasan gaba na Palmeiras Endrick duk da cewa tuni Paris St-Germain ta taya matashin dan Brazil din mai shekara 16.
Sampdoria ka iya soke aron da ta dauko Harry Winks na shekara daya daga Tottenham tun kafin wa’adi, tun da dan wasan na tsakiya na Ingila har yanzu bai taka mata leda ba saboda ciwon idon sawu.
Dan wasan tsakiya na Najeriya Alex Iwobi, na shirin kulla sabuwar yarjejeniyar shekara uku da rabi da Everton, inda za ta rika biyansa fam dubu daya a mako.
Everton za ta iya barin dan bayanta na Colombia Yerry Mina, da dan wasanta na tsakiya Abdoulaye Doucoure, na Mali idan wata kungiya ta taya su a watan Janairu.
Hukumomin gasar Premier ba za su bi sabon tsarin hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa, ba, idan aka koma gasar bayan Kofin Duniya, na kara lokacin da aka bata a wasa inda ake ganin wasu wasannin da ake yi yanzu a Qatar na kaiwa sama da minti 100.
Manchester United na duba yuwuwar zawarcin dan wasan Bayer Leverkusen Moussa Diaby na Faransa.
West Ham za ta sayar da dan bayanta Vladimir Coufal a watan Janairu, idan ta samu tayin da ya kai fam miliyan 6 a kan dan kasar Czech din.
Attajirin nan mai katafaren kamfanin tufafi da kayan kawa, Zara, Amancio Ortega, ba shi da sha’awar sayen Manchester United, duk da rahotannin da aka yada a baya cewa dan kasuwar mai shekara 86 a shirye yake ya yi taya kungiyar.
Kociyan Barcelona Xavi Hernandez ya bukaci kungiyar ta kara tsawon kwantiragin dan wasansa na tsakiya Sergio Busquets na Sifaniya da shekara daya.
Real Betis na duba yuwuwar sayen Adama Traore, na Sifaniya wanda kwantiraginsa a Wolves zai kare a karshen kaka.
Tsohon dan bayan Arsenal da Manchester City Kolo Toure, mai shekara 41, ya amince da yarjejeniyar shekara uku da rabi ta zama kociyan Wigan.