Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wasanni 10 na kofin duniya da suka bayar da mamaki
Saudiyya ta bai wa duniya mamaki bayan da ta yi nasara kan Argentina da ƙwallo biyu a wasan cin Kofin Duniya na rukunin C a birnin Lusail na Qatar.
Argentina ta lashe gasar sau biyu a tarihi.
Da alama an zata wasa ya ƙare tun kafin a je rabin lokaci bayan da Argentina ta zura ƙwallo ɗaya ta hannun ɗan wasanta Lionel Messi, sai kuma ƙwallaye uku da Argentina ɗin ta jefa, waɗanda alƙalin wasa ya ce an yi satar-fage.
Sai dai wasan ya sauya a cikin minti 10 bayan dawowa daga hutun rabin lokaci, Saleh Al-Shehri ne ya rama wa Saudiyya, yayin da Salem Al Dawsari ya ci ƙwallo ta biyu, abin da ya sanya magoya baya suka yi ta sowa.
Irin wannan wasa mai ban mamaki sukan ƙara wa gasar kofin duniya armashi.
Shin waɗanne wasanni ne aka samu a baya irin wannan?
Masu gabatar da shiri na BBC Gary Lineker, da Alan Shearer da kuma Micah Richards sun tattauna kan wannan batu.
Koriya ta kudu 2-1 Italiya (Richards: 7, Shearer: 10)
Koriya ta kudu ta doke Italiya da ƙwallo biyu da ɗaya a zagayen ƙasashe 16 na gasar kofin duniya ta 2002, lokacin da ta kai matakin kusa da na ƙarshe.
Ahn Jung-hwan, wanda ya kwashe kakar wasannin da ta gabaci lokacin gasar a matsayin ɗan wasan aro a ƙungiyar Perugia ne ya zura ƙwallon da ta fitar da Italiya, wadda take da shahararrun ƴan wasa kamar Gianluigi Buffon, da Pablo Maldini, da kuma Alessandro del Piero.
Netherlands 5-1 Sifaniya 2014 (Richards: 10, Shearer: 7)
Sifaniya ta fara kokarin kare kambinta a gasar kofin duniya ta 2014 da ƙafar hagu lokacin da Netherland ta sharara mata ƙwallaye biyar a karawar farko na rukuni a gasar, wadda aka buga a Brazil.
Inda Netherlands ta rama doke ta da Sifaniya ta yi a wasan ƙarshe na gasar a 2010. Wannan shan ƙasa mafi muni da wata ƙasa mai kare kambinta ta taɓa yi a gasar cin kofin duniya.
Gabashin Jamus 1-0 Yammacin Jamus 1974 (Richards: 6, Shearer: 9)
An yi tunanin cewar ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Yammcin Jamus, wadda kyaftin ɗinta Franz Beckenbauer ke wa jagoranci, wadda kuma ta ƙunshi ƙwararren ɗan wasan gaba Gerd Muller su ne za su yi nasarar a kan Gabashin Jamus, musamman kasancewar su ne ke karɓar baƙuncin gasar kuma su ne suka lashe gasar kofin nahiyar Turai.
To amma ƙwallon da Jurgen Sparswasser ya saka ana gab da tashi ita ce ta tabbatar da nasarar Gabashin Jamus, abin da ya sanya suka zo matsayi na ɗaya a rukunin.
Senegal 1-0 Faransa 2002 (Richards: 4, Shearer: 8)
Wani wasan farko da ya bai wa kowa mamaki inda aka yi nasara a kan zakarun duniya.
Ƙwallon da Papa Bouba Diop ya ci ita ce ta bai wa Senegal nasara, a gasar da aka buga a Korea/Japan 2002, kuma karon na farko ke nan da Senegal ta je gasar.
Senegal ta kai har zagayen ƙasashe takwas, yayin da Faransa kuwa ta fice daga wasan bayan da ta zo na ƙarshe a rukunninta da maki ɗaya a wasa uku.
Scotland 3-2 Netherlands 1978 (Richards: 9, Shearer: 3)
Archie Gemmil ne ya zura ɗaya daga cikin ƙwallaye mafi burgewa a tarihin kofin duniya, wadda ta taimaka wa Scotland bai wa Netherlands mamaki a gasar cin kofin duniya ta 1978 a Argentina.
Ana minti 20 kafin a tashi wasa Scotland ce ke kan gaba 2-1, daga nan sai Gremmil ya ratsa masu tsaron baya uku na Netherlands kafin zura ƙwallo a raga duk da koƙarin mai tsaron gida Jan Jongbloed.
Sifaniya 0-1 Switzerland 2010 (Richards: 8, Shearer: 4)
Sifaniya ta je gasar kofin duniya ta 2010 a matsayin zakarun kofin ƙasashen Turai, to amma ba su fara gasar wadda aka buga Afirka ta Kudu da sa'a ba, inda suka yi rashin nasara a hannun Switzerland da ci ɗaya, daga tsohon ɗan wasan Manchester United Gelson Fernandes.
Amurka 1-0 Ingila 1950 (Richards: 1, Shearer: 6)
Ingila ta isa Brazil don buga Gasar Kofin Duniya ta 1950 a matsayin waɗanda ake ganin za su ci kofin, kuma an yi tunanin za su bige Amurka kwaf ɗaya saboda rashin ƙwararrun 'yan wasa.
Sai dai Haifaffen Haiti Joe Gaetjens, akanta kuma mai wanke-wanke a gidan cin abinci da ke Brooklyn, shi ne ya ci ƙwallon ɗaya tilo da ta ba su nasara.
Argentina 0-1 Kamaru 1990 (Richards: 2, Shearer: 5)
Shekara huɗu bayan Diego Maradona ya jagoranci ƙasarsa a cin Kofin Duniya tsakaninsu da Mexico, Argentina suka sha mamaki a wasan farko na gasar a Italiya a Filin Wasa na San Siro.
Ƙwallon da Francois Omam-Biyik ya ci da ka ce ta bai wa Kamaru nasara, bayan an bai wa 'yan wasansu Andre Kana-Biyik da Benjamin Massing jan kati.
Sifaniya 0-1 Ireland ta Arewa 1982 (Richards: 5, Shearer: 1)
Mutane kaɗan ne suka zaci Ireland za ta ci wasan a lokacin da suka take wasa da masu masaukin baƙi Sifaniya a wasan ƙarshe na rukuni, tana mai neman nasara kafin su je zagaye na gaba.
Sai dai ƙwallon da Gerry Armstrong ya ci a farkon falle na biyu na wasan ta ba da mamaki sosai saboda sun buga akasarin falle na biyu na wasan da mutum 10 a cikin fili bayan an kori Mal Donaghy.
Italiya 0-1 Koriya ta Arewa 1966 (Richards: 3, Shearer: 2)
Italiya wadda ake kallon za ta lashe kofin a 1966, ta je Filin Wasa na Ayresome Park da zimmar ta samu canjaras a wasanta da Koriya ta Arewa don tsallakawa zagayen 'yan 16.
Sai dai ƙwallon da Pak Doo-ik ya ci ta kai Koriya zagaye na gaba a madadin Italiya, wadda ta fita daga gasar a kunyace.