Real Madrid ta caskara Real Valladolid a La Liga

Real Madrid

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Real Madrid ta doke Real Valladolid 3-0 a wasan mako na biyu a La Liga ranar Lahadi a Santiago Bernabeu.

Ƙungiyoyin sun kammala minti 45 ɗin farko, ba tare da zura ƙwallo ba a raga, inda sai a zagaye na biyu ne Real ta ci ƙwallayen.

Aminti na 50 ne ƙungiyar da take rike da Uefa Super Cup na bana ta fara cin ƙwallo ta hannun Valverde, sai Brahim Díaz ya kara na biyu, sannan Endrick ya ci na uku.

Karo na biyu a jere Kylian Mbappe bai ci wa Real Madrid ƙwallo ba, wanda daga baya aka sauya shi da Endrick, wanda ta ɗauka a bana.

Mbappe, wanda ya ci ƙwallo a Real Madrid a Uefa Super Cup da ta doke Atalanta a watan nan, ya koma Santiago Bernabeu daga Paris St Germain kan fara kakar bana.

Wannan shi ne wasan farko da Real ta buga a gida, bayan da ta je ta tashi 1-1 a makon farko a La Liga a gidan Mallorca.

Real Madrid ta zura ƙwallo takwas a ragar Valladolid a La Ligar a 2022/23, inda ta je ta ci 2-0 ranar 30 ga watan Disambar 2022, sannan ta zura 6-0 ranar 2 ga watan Afirilun 2003 a gida.

Ranar Alhamis 29 ga watan Agusta, Real za ta je Las Palmas, domin buga wasan mako na uku a babbar gasar tamaula ta Sifaniya.

Kafin nan Real Valladolid za ta karbi bakuncin Leganes ranar Laraba 28 ga watan Agusta a gasar ta La Liga.

Kafin a fara wasan sai da aka yi shiru na minti ɗaya, domin tuna ƴan wasan Real da na Valladolid da ma'aikata da suka mutu a kakar da ta wuce.

Haka kuma Real ta yi jimamin mutuwar tsohon mataimakin shugaba a 1995 kuma mambanta na tsawon shekara 43, Juan Miguel Villar Mir da ɗan wasan Real Madrid, Eduardo Chato González, wanda ya buga wa ƙungiyar tamaula daga 1966 zuwa 1969, wanda a lokacin ya lashe kofin lik uku.

Haka itama Valladolid ta yi jimamin mutuwar Francisco García Gómez Paquito, tsohon ɗan wasan Sifaniya, wanda ya yi mata koci, sannan ya horar da Real Valladolid.