Man United za ta sayar da Kambwala ga Villareal

An wallafa

Manchester United ta amince za ta sayar da mai tsaron bayan, Willy Kambwala ga Villarreal ta Sifaniya.

Wata majiya daga United ta ce ƙungiyar da ke Old Trafford za ta karɓi £4.63m, idan aka haɗa da karin tsarabe-tsarabe ƙudin zai kai £9.68m.

A ƙunshin yarjejeniyar da suka ƙulla, United za ta iya sake sayen matashin ɗan wasan mai shekara 19, idan tana da bukatar hakan.

Kambwala zai je Sifaniya, domin a auna koshin lafiyarsa nan gaba, sai maganar saka hannu kan ƙunshin yarjejeniya nan da kwanaki masu zuwa.

Saura kaka ɗaya yarjejenjiyar matashin ɗan ƙwallon tawagar Faransa ya kare a United, wanda bai yadda ya tsawaita ƙwantiraginsa ba, duk da tayin da aka yi masa.

Kambwala ya buga wasa 10 a kakar da ta wuce a United, bayan da Erik ten Hag ya bashi dama, sakamakon da ƙungiyar ta yi fama da ƙarancin masu tsare baya.

United ta yi fama da masu tsare mata baya da suka dunga yin jinya sosai a kakar da ta wuce.

Ƙungiyar Old Trafford za ta buga Europa League a kakar bana, bayan da ta lashe FA Cup a kakar da ta kare.