Ko daga ina gahawa abin da aka fi sha a duniya ya samo asali?

Asalin hoton, Getty Images
Daga manyan titunan birnin New York zuwa tsaunukan Habasha, gahawa ya kasance wani muhimmin abin sha na yau da kullum ga miliyoyin mutane.
Shan gahawar ya kasance wani abin al'ada fiye da ƙarni goma sha biyar, inda wasu ke danganta tasirinsa da kuma wayar da kai a ƙarni na 17 da 18, lokacin da aka kafa tushen da yawa daga cikin ra'ayoyin tunani da al'adu na wannan zamani.
Babban abin da ake hada gahawa da shi, shi ne sinadarin caffeine, wanda a yanzu ana la'akari da shi a matsayin wanda aka fi shansa a duniya, inda yake tasiri kan yadda muke tunani da kuma ji.
Daga ina gahawa ya samo asali?
Gahawa dai ya samo asali ne daga 'ya'yan itacen gahawa na arabica, wanda aka fara ganowa a Habasha.
Ana noman fiye da kashi 90 na gahawa a ƙasashe masu tasowa, musamman a Kudancin Amurka da kuma a Vietnam da Indonesiya, yayin masu shansa kuma galibi ke a ƙasashe masu karfin tattalin arziki.
Wani mai suna Legend, ya ce a cikin karni na 9, wani makiyayi mai suna Kaldi ya lura da ƙaruwar karfin awakinsa bayan sun ci 'ya'yan itace na gahawa, wanda ya sa ya gwada su da kansa.
Daga nan ne jama’ar garin suka fara shan waken ’ya’yan itace ko kuma yin shayi da ganyen itacen.
Litattafan tarihi sun nuna cewa Sufaye a Yemen ne suka fara gasa iri na gahawa a ƙarni na 14, inda suka ƙirƙiri abin sha da muka sani a yau.
A ƙarni na 15, gidajen shan gahawa sun bayyana a faɗin Daular Usmaniyya, daga baya suka bazu zuwa Turai inda suka zama cibiyar kasuwanci, siyasa da kuma samar da sabbin bayanai.

Asalin hoton, Getty Images
Wasu manazarta, kamar Jürgen Habermas, fitaccen masanin falsafa ɗan ƙasar Jamus kuma masanin zamantakewa na karni na 20, ya kalubalanci cewa wayar da kai ɗin da aka yi da ba zai faru ba in ba da taimakon gahawa ba.
A cewar Habermas, gidajen shan gahawa sun zama "cibiyoyin suka" a cikin ƙarni na 17 da 18 inda aka kirkiro da ra'ayoyin jama'a da kuma bayanai.
An yi imanin cewa manyan jiga-jigan wayewa su ma sun kasance manyan masu sha'awar gahawa.
Masanin falsafa ɗan ƙasar Faransa, Voltaire, yana shan kofin gahawa guda 72 a rana yayin da takwaransa Diderot ya dogara da shi wajen haɗa wani kundinsa na ilimi mai suna "Encyclopédie", wanda ake kallon sa a matsayin ka'idar aikin wayar da kai, a cewar marubucin Ba'amurke, Michael Pollan.

Asalin hoton, Getty Images
Farfesa Ted Fischer wanda ke jagorantar Cibiyar Nazari kan Gahawa a Jami'ar Vanderbilt ta Amurka, ya ce gahawa ya kuma taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa tsarin jari-hujja.
Ya shaida wa BBC cewa: "Gahawa ya canza tarihi kuma ya karfafa ra'ayoyin da suka haifar da Faɗakarwa da jari-hujja.
"Ba wai kamar wani hatsari ne kawai a gare ni ba, cewa ra'ayoyi game da dimokuraɗiyya, kimiyya da jari-hujja sun zo ne a lokacin da amfani da shi ya zama sananne. Wannan abu, wanda ke faɗaɗa fahimta da kuma mayar da hankali, hakika yana cikin abubuwan da suka kai ga haifar da jari-hujja."
A lokacin, ’yan kasuwa sun fahimci cewa za a iya amfani da gahawa don haɓaka yawan aiki, Fischer ya ƙara da cewa, don haka suka fara ba da ganyen gahawa ga ma’aikatansu kuma daga ƙarshe suka bar su su rika zuwa suna shna gahawa.
Wani ɓangare na rashin amfanin gahawa
Tarihin gahawa ba zai kammalu ba, ba tare da an bayyana wani ɓangare na rashin amfaninsa ba, saboda ya taka rawa wajen cin zarafin bayi.
Faransa ta yi amfani da bayi daga Afirka wajen noman gahawa a Haiti kuma a farkon shekarun 1800 Brazil na samar da kashi uku na gahawa da ake sha a duniya ta hanyar amfani da bayin Afirka.
A yau, gahawa shi ne ginshiƙin al'adu a duniya, inda ake shan kofinsa fiye da biliyan biyu a kullum, inda kuma yake samar da dalar Amurka biliyan 90 a kowace shekara.
Duk da haka, "abu kaɗan ne ya canza" a cikin shekaru 600, a cewar wata ƙungiya Heifer International wadda ke aiki don kawar da talauci da yunwa a duniya.
Ta ce mutane masu launi sun kasance kashin bayan masana'antar gahawa, suna aiki don samu na kansu. A faɗin ƙasashe 50, mutane miliyan 125 ne suka dogara da gahawa don ayuwa, inda sama da rabi ke rayuwa cikin talauci.
Ta yaya gahawa ke shafar jiki?
Idan aka sha sinadarin Caffeine, yana narkewa kuma yana shiga cikin jini da hanjin mutum.
Tasirinsa na farawa ne da zarar ya isa kwakwalwa.
Wannan ya faru ne saboda kamannin sinadarai na maganin caffeine da adenosine, wani abu da jiki ke samarwa a zahiri. Adenosine yawanci yana haifar da raguwar bugun zuciya da haifar da jin bacci da annashuwa.
Yana iya haifar da hawan jini, ta da aikin kwakwalwa, rage jin yunwa da kuma mai da hankali na tsawon lokaci.

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Har ila yau, tasirin sinadarin caffeine yana haɓaka yanayi, rage gajiya, da saka kwazon aikin kuma wasu lokuta 'yan wasa suna amfani da su don karin kuzari.
Wannan tasiri na iya kai wa tsawon mintuna 15 zuwa sa'o'i biyu. Jiki yana cire caffeine sa'o'i biyar zuwa 10 bayan shansa, amma tasirinsa na iya daɗewa.
Don haɓaka amfanin sinadarin caffeine, masana suna ba da shawarar shan shi cikin matsakaici da kuma guje wa shan shi da rana don kiyaye tasirinsa lokacin da aka fara shan gahawa a rana ta gaba.
Sun kuma ba da shawarar cewa a rika mutanen da suka balaga su rika shan caffeine da bai wuce miligram 400 ba a kowace rana, wanda ya yi daidai da kofuna huɗu ko biyar na gahawa.
Yayin da ra'ayoyi suka bambanta, zarce wannan adadi zai iya haifar da sakamako mara kyau kamar rashin barci, damuwa, bugawar zuciya da sauri, ciwon ciki, tashin zuciya da kuma ciwon kai.
Kwararru daga Hukumar Abinci da Magunguna ta Amurka sun yi gargaɗin cewa illolin masu guba, kamar kamewar jijiyon kwakwalwa, na iya faruwa ga masu shan shan miligram 1,200 na sinadarin caffeine - kusan kofuna 12 na gahawa.
Ana tunanin cewa gahawa na da amfani ga lafiya kuma yana da alaƙa da rage haɗarin mutuwa da cututtuka da yawa, a cewar Dr Mattias Henn daga Makarantar Kiwon Lafiyar Jama'a, Harvard TH. Chan.
Ya shaida wa BBC cewa: "Shan kofi biyu zuwa biyar na gahawa a rana yana da alaka da raguwar haɗarin mace-mace, amma har da ciwon suga, cututtukan zuciya da ma wasu nau'ukan ciwon daji."
Don haka lokaci na gaba da kuka buƙaci shan gahawa, kuna iya yin tunani kan tarihin da ke tattare da samar da shi.











