Newcastle ta kusa daidaitawa da Elanga, Real Madrid za ta cefanar da Rodrygo

Asalin hoton, Getty Images
Newcastle ta yi tayin fam miliyan 55 kan ɗanwasan Sweden Anthony Elanga mai shekara 23 kuma sun kusa ƙulla yarjejeniya da Nottingham Forest. (Mail)
Real Madrid da koci Xabi Alonso sun amince kan cefanar da ɗanwasan gaba na Brazil Rodrygo, wanda ake alaƙanta shi da Arsenal, idan aka samu tayi mai gwaɓi kan ɗanwasan mai shekara 24. (Athletic - subscription required)
Fenerbahce ta yi tayin Euro miliyan 15, kwatankwacin fam miliyan 12.9 kan ɗanwasan gaba na Paris St-Germain Marco Asensio, sai dai ɗanwasan mai shekara 29 yana dakon wasu damarmakin yayin da AC Milan da Villareal ke zawarcin ɗanwasan na Sifaniya. (L'Equipe - in French)
Como ta amince da tayin fam miliyan 16.5 kan ɗanwasan Celtic Nicolas Kuhn mai shekara 25. (Sky Sports)
Rangers na dab da kammala ƙulla yarjejeniya kan ɗanwasan Luton Town ɗan asalin Norway Thelo Aasgaard mai shekara 23. (Daily Record)
Tottenham Hotspur da Chelsea na daga cikin ƙungiyoyin da ke rige-rigen sayen ɗanwasan AZ Alkmaar Kees Smit mai shekara 19. (TBR Football)
Al-Nassr na iya karkatar da hankalinta ga ɗanwasan Arsenal Gabriel Martinelli mai shekara 24 bayan gwagwarmayar da suka yi kan ɗanwasan Liverpool Luis Diaz mai shekara 28. (GiveMesport)
Ɗanwasan Portugal Antonio Silvia mai shekara 21 ya yi watsi da batun komawa Al Hilal ta Saudiyya sai dai har yanzu ana sa ran ɗanwasan zai bar Benfica. (A Bola - in Portuguese)
Kocin ƴan ƙasa da shekara 21 na Arsenal Mehmet Ali ya raba gari da ƙungiyar inda ya koma Brentford. (Football London)














