Arsenal ta dage kan zawarcin Rodrygo, Manchester United ta yi wa Sancho farashi

Asalin hoton, Getty Images
Arsenal ta samu ƙwarin gwiwa kan zawarcin da ta ke yi wa ɗan wasan gaban Brazil, Rodrygo, wanda ba shi da tabbacin samun gurbi a tawagar farko ta Real Madrid ƙarƙashin sabon koci Xabi Alonso. (Mirror)
Manchester United na neman aƙalla fam miliyan 25 kan Jadon Sancho, mai shekara 25, yayin da Juventus ke ci gaba da zawarcin ɗan wasan na Ingila. (Corriere dello Sport)
Sancho ya shirya rage albashin sa don komawa ƙungiyar da ta lashe gasar Serie A sau 36. (Eurosport Italia)
Atletico Madrid a shirye take ta yi duk mai yiwuwa don siyan ɗan wasan bayan Tottenham da Argentina Cristian Romero, mai shekara 27, inda ta ke da niyyar biyan fam miliyan 61 kan ɗan wasan. (AS)
West Ham ta yi watsi da tayin fam miliyan 50 daga Tottenham kan ɗan wasan gaban Ghana Mohammed Kudus, mai shekara 24. (Talksport).
Manchester United na ƙara matsa ƙaimi a zawarcin da ta ke yi wa ɗan wasan gaban Aston Villa da Ingila Ollie Watkins, mai shekara 29, kuma ta fara tattaunawa da kulob ɗin na yankin Midlands wanda ke son fam miliyan 60 a kan ɗan wasan. (Mirror)
Kocin Napoli Antonio Conte na son ɗaukar ɗan wasan Najeriya Ademola Lookman, mai shekara 27, daga Atalanta a wannan bazarar. (La Gazzetta dello Sport)
Newcastle na shirin ƙulla yarjejeniya da golan Burnley da Ingila James Trafford, mai shekara 22, nan da mako mai zuwa, kuma za ta ci gaba da tattaunawa da Nottingham Forest kan ɗan wasan Sweden Anthony Elanga, mai shekara 23. (i paper)
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ɗan wasan gefe na ƙasar Japan Kaoru Mitoma, mai shekara 28, ya shaida wa Brighton cewa yana son ci gaba da zama a ƙungiyar da kuma sanya hannu kan wata sabuwar yarjejeniya duk da ana alaƙanta shi da Bayern Munich. (Sky Sports)
Golan Nice Marcin Bulka, mai shekara 25, na shirin komawa ƙungiyar Neom ta gasar Saudi Pro League, duk da cewa Sunderland ta gabatar da tayin fam miliyan 12.8 kan ɗan wasan na Poland. (Meczyki)
Sunderland ta mayar da hankalinta kan sayen golan Chelsea ɗan ƙasar Serbia Djordje Petrovic, mai shekara 25, amma tana fuskantar hamayya daga Aston Villa da Bournemouth. (Times)
Ɗan wasan gaba na Italiya Ciro Immobile, mai shekara 35, zai soke kwantiraginsa da Besiktas na Turkiyya ya koma Bologna a kyauta. (Corriere dello Sport)
Ɗan wasan baya na Valencia ɗan ƙasar Sifaniya Cristian Mosquera, mai shekara 21, ya ƙi amincewa da sabon kwantaragi mai tsoka da kulob ɗin na La Liga saboda ya na son ya koma Arsenal. (Las Provincias)











