Abu takwas da bai kamata a yi a kusa da gas ba

Wata mata na kirgi da gas

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Aisha Babangida
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Broadcast Journalist
    • Aiko rahoto daga, BBC News, Abuja
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 4

A gidajenmu da dama, musamman a birane, amfani da gas ya maye gurbin itace da rusho saboda gas ya kasance ɗaya daga cikin abubuwan da ke sauƙaƙa rayuwar yau da kullum.

Duk da haka, rashin bin ƙa'idojin tsaro wajen amfani da gas na iya haifar da mummunar gobara ko fashewa da zai iya haddasa rasa rayuka ko dukiyoyi.

Wannan ya sa BBC ta tattauna da Tijjani Muhammad Abba, tsohon mataimakin shugaban hukumar kashe gobara domin ya yi mana bayani kan abubuwan da bai kamata a yi a kusa da gas ba, da kuma matakan kariya da ya kamata mu bi.

Tijjani ya bayyana cewa mutane da yawa suna sakaci da gas, alhali ba ya buƙatar sakaci ko raini.

A cewarsa: "Shi gas yana buƙatar a mutunta shi. Ba a manaji a harkar gas, kuma ƙazanta da sakaci ne ke jawo haɗarin gobara."

Waɗanne abubuwa ne bai kamata a yi ba kusa da gas?

...

Asalin hoton, Getty Images

Akwai abubuwa da dama da bai kamata a yi ba a kusa da gas in ji Tijjani, kuma sun haɗa da;

  • A guji amfani da wayar hannu

Tsohon mataimakin shugaban hukumar kashe gobarar ya ce a guji amfani da wayar hannu ko kunna sigari a kusa da gas

Ƙaramar wuta daga waya ko sigari na iya haifar da gobara mai girma, a cewar tsohon babban jami'in a hukumar kashe gobara.

  • Kada a ajiye abubuwan fashewa a kusa
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Tijjani Muhammad Abba ya ce kada a ajiye abubuwan fashewa kusa da gas

''Bai kamata a kusantar da abubuwa kamar sun man fetur, turaren wuta, maganin feshi, da sinadarai masu ƙonewa kusa da gas ba'', kamar yadda ya yi arin haske.

  • Hana yara zuwan kusa da gas

Tsohon mataimakin shugaban hukumar kashe gobarar ya ce kada a bar yara suna wasa kusa da gas ko cikin ɗakin girki.

''Yara ba su da fahimtar haɗari, saboda haka yin wasa a kusa da gas na iya haifar da hatsari in ji shi,'' in ji shi.

  • Rashin kashe gas idan za a fita

Tsohon jami'in kashe gobarar ya ce bai kamata a bar wutar gas tana ci ba tare da kowa a kitchen ba

''Sakaci da wuta a kitchen na iya zama sanadin gobara idan wani abu ya faru'', in ji shi.

  • Kada a rufe kitchen gaba ɗaya idan ana amfani da gas

Tijjani Muhammad Abba ya ce bai kamata a rufe kichin ruf ba, matsawar ana amfani da gas a ciki.

''Iska mai shiga da fita na taimakawa wajen hana taruwar hayaƙi ko warin gas'', in ji shi.

  • Kada a ajiye tukunyar gas a cikin ɗakin girki.

Masanin hatsarin gas ɗin ya ce bai kamata a riƙa ajiye tukunyar gas a cikin ɗakin girki ba.

''Ya fi kyau a ajiye tukunyar gas a waje, a kewayeta da waya ko gini don rage haɗari'', in ji shi.

  • Kada a kunna ko kashe lantarki idan an ji warin gas

Tsohon mataimakin shugaban hukumar kashe gobarar ya ce a guji kunna wutar lantarki ko kasheta a lokacin da aka ji warin gas.

''Ƙaramar walƙiya daga na'urar lantarki kaɗai na iya haddasa gobara'', a cewarsa.

  • A guji ajiye tukunyar gas ɗin da ke yoyo a gida

Masanin ya kuma yi gargaɗin ajiye tukunyar gas mai yoyo a gida, saboda hatsarin da ke tattara da ita.

''Da zarar an fahimci tukunyar gas tana yoyo, a kai gurin da za a iya dubawa a gano matsalar, sai a gyara shi''.

Ya ƙara da cewa ''Idan ta tsufa ko ta tsage, a sauya ta domin guje wa zubewar iskar gas''.

Matakan kariya

...

Asalin hoton, Getty Images

Tsohon matakin shugaban hukumar kashe gobarar ya ce akwai abubuwan da ya kamata mutane su yi domin kariya daga gobara wajen amfani da gas, su ne

  • Duba tukunyar gas akai-akai
  • Tabbatar da wadataccen iska a wurin girki
  • Ajiye abin kashe gobara a kusa da ɗakin girki.
  • Rufe bawul ɗin gas bayan amfani
  • Koyar da 'yan gida yadda ake amfani da gas
  • Tsafta da kulawa

A tabbatar da tsafta a wurin ɗakin girki, kuma a hana yara shiga wurin dafa abinci ko wurin da aka ajiye gas suna wasa.

Gas kayan taimako ne mai muhimmanci da ke sauƙaƙa rayuwa, amma rashin bin ƙa'idojin tsaro na iya zama sanadin asarar dukiya ko rayuka.

Saboda haka ne Tijjani Muhammad Abba ya jaddada cewa a ɗauki tsaro a matsayin muhimmin abu wajen amfani da gas, domin haɗarinsa ya fi na man fetur.