Me zai faru a wasannin Champions League ranar Talata

Champions League

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Za a buga wasa huɗu ranar Talata a Champions League karawar cike gurbi, domin fitar da waɗanda za su kai zagayen ƴan 16.

Za a kara tsakanin Brest da Paris Saint-Germain da na Juventus da PSV Eindhoven da na Sporting da Borussia Dortmund da na Manchester City da Real Madrid.

Wasannin da za a buga ranar Talata 11 ga watan Fabrairu

  • Brest da Paris Saint-Germain
  • Juventus da PSV Eindhoven
  • Manchester City da Real Madrid
  • Sporting da Borussia Dortmund

Za a yi karawa huɗu ranar Talata da kuwa wasu huɗun ranar Laraba, domin ware takwas ɗin da za su ci gaba da karawar ƴan 16.

Tun farko an ware takwas ɗin farko da suka kai zagayen gaba kai tsaye a sabuwar fasalin gasar Champions League da tsarin ya fara daga kakar nan.

Brest da Paris St Germain

Dembele

Asalin hoton, Getty Images

Brest za ta kara a zagayen cike gurbi, sakamakon da ta yi ta 18 a Champions League, bayan cin wasa huɗu da canjaras uku da rashin nasara ɗaya.

Ita kuwa Paris St Germain ta 15 ta kammala a teburi, bayan wasa takwas a cikin rukuni, wadda ta ci karawa huɗu da canjaras ɗaya sannan ta yi rashin nasara uku.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Wasa ne tsakanin ƙungiyoyin Faransa na Ligue 1, PSG ta doke Brest 8-3 gida da waje a bana a babbar gasar tamaula ta Faransa.

PSG ce ta daya a kan teburi da maki 53 da tazarar maki 10 tsakani da Marseille ta biyu - Ita kuwa Brest mai maki 31 tana ta takwas din teburi a bana.

PSG na fatan taka rawar da za ta kai zagayen ƴan 16, tana kuma sa ran Ousmane Dembele zai sa ƙwazo, wanda ya zama na farko a ƙungiyar da ya ci uku rigis a wasa biyu a jere.

Dembele ya ci uku rigis a wasan da PSG ta je ta doke Stuttgard a Champions League a Jamus a wasan da suka yi nasara 4-1 ranar Laraba 29 ga watan Janairu.

Haka kuma ya kara cin uku rigis a karawar da PSG ta je ta doke Brest 5-2 a Ligue 1 ranar Asabar 1 ga watan Fabrairu.

Ya kuma zura biyu a ragar Monaco a wasan Ligue 1 da PSG ta yi nasara 4-1 ranar Juma'a 7 ga watan Fabrairu.

Wannan shi ne karo na biyu da ƴan Faransa za su fuskanci juna a irin wannan lokacin a Champions League.

Na farkon shi ne a 2009/10 tsakanin Lyon da Bordeux.

Juventus da PSV Eindhoven

Champions League

Asalin hoton, Getty Images

Juventus ta kawo wannan matakin, bayan da ta kare a matsayi na 20, wadda ta ci wasa uku da canjaras uku da rashin nasara biyu.

Ita kuw PSV ta 14 ta karkare, wadda ta yi nasara huɗu da canjaras biyu da rashin nasara biyu daga karawa takwas a cikin rukuni.

A wasan farko a cikin rukuni a gasar ta zakarun Turai, Juventus ta doke PSV 3-1 a cikin watan Satumba.

To sai dai PSV ta kawo wannan gurbin, sakamakon doke Liverpool 3-2 a Eindhoven a wasan karshe a cikin rukuni.

Ita kaɗai ce ta ci Liverpool a Champions League a gasar bana, wadda ƙungiyar da ke buga Premier League ta lashe wasa bakwai da ta fuskanta.

Manchester City da Real Madrid

Champions League

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Clement Turpin shi ne zai busa wasan City da Real - karo na takwas da zai yi alkalancin wasa da Real Madrid

Manchester City ta kawo wannan matakin, sakamakon da ta yi ta 22 a teburi, wadda ta ci wasa uku da canjaras biyu aka doke ta karawa uku.

Real Madrid ta 11 ta yi, bayan nasara biyar aka doke ta fafatawa uku.

Duk ƙungiyar da ta yi nasara a wasa uku baya da suka fafata, ita ce ke lashe Champions League.

Real Madrid ta ɗauki kofin zakarun Turai na 14 a 2021/22, sakamakon nasara a kan City da kuma na 15 da ta lashe a 2023/24.

Ita kuwa City ta ci Champions League a karon farko a tarihi a kakar 2022/23, sakamakon doke Real Madrid a zagayen daf da karshe.

Wannan ne karo na 13 da za su kece raini a tsakaninsu, inda Real Madrid ta yi nasara uku da canjaras biyar, City ta ci huɗu daga ciki.

Sporting da Borussia Dortmund

Borussia Dortmund

Asalin hoton, Getty Images

Sporting za ta buga wasa mai zafi da Borussia Dortmund ranar Talata, bayan da ƙungiyar Jamus ta kai gurbin gaba da tashi 1-1 da Bologna a cikin rukuni a Champions League.

Sporting ta kare a mataki na 23 a teburin gasar zakarun Turai, wadda ta yi nasara uku da canjaras biyu da rashin nasara biyu.

Ita kuwa Dortmund ta ci wasa biyar da canjaras uku, wadda ta yi ta 10 a teburin Champions League gasar da aka canja wa fasali daga kakar nan.

Dortmund za ta je Sporting da sabon koci, Nico Kovac, bayan da ya maye gurbin Nuri Sahin, wanda ta sallama a cikin watan Janairu.

Kenan wasa na biyu da Kovac zai ja ragamar Dortmund kenan, bayan fafatawa da Stuttgard ranar Asabar a Bundesliga

Sporting ce ta kai zagayen gaba a Champions League a Nuwambar 2021 da suka fafata, kafin nan Dortmund ce ta yi nasara haɗuwa uku a kan ta Portugal.

Wannan shi ne wasa na biyar da za su fafata a gasar ta zakarun Turai, Dortmund ta yi nasara uku, Sporting ta ci wasa ɗaya.