Zan gabatar da kudirin binciken PENGASSAN - Ndume

Asalin hoton, Twitter
Wasu yanmajalisar dattawan Najeriya sun ce za su gabatar da kudiri na neman sake diba dokar ƙwadago a ƙasar bayan rikicin ƙungiyar manyan ma'aikatan kamfanonin iskar gas da fetur ta PENGASSAN da matatar mai ta Dangote.
A ranar Laraba ne ne ƙungiyar PENGASSAN ta janye yajin aikin da ta shiga saboda adawa da matakin matatar Dangote na korar wasu ma'aikatanta kimanin 800.
Matatar Dangote ta ce ta ɗauki matakin sake fasalta tsarin ma'aikata me saboda bukatu na aiki ba tare da alaka da ayyukan wata kungiya ba.
Sanata Ali Ndume daga jihar Borno ya ce duk da an samu maslaha tsakanin bangarorin biyu amma "rikicin ya yi mummunan tasiri ta hanyar jefa yan Najeriya cikin wahala, don haka akwai bukatar sake diba dokar tare da yin gyara."
"Farashin mai ya tashi daga 890 zuwa 900, an ci zarafin ƴan Najeriya kusan 200," in ji Ndume.
Kamfanin mai na NNPCL a Najeriya ya ce yajin aikin kungiyar PENGASSAN na kwana uku ya janyo wa Najeriya hasara na raguwar man da kasar ke samarwa da kashi 16, da kuma hasarar kashi 30 na kasuwar hada-hadar iskar gas.
Sanata Ali Ndume ya ce dole majalisa ta gudanar da bincike tare da diba bukatar yin gyara ga dokar ƙwadago a Najeriya.
"Na sa a duba min yadda zai kasance ba a cutar da PENGASSAN ba kuma ba su yi amfani da damar da aka ba su ƙarƙashin doka kamar yadda suka yi ba a yanzu domin sun ci zarafin talakawa."
"Za mu sake duba dokar a yi gyara yadda ya kamata," A cewar Ndume.
Sanatan ya ce shi yana ganin kotu ya kamata ƙungiyar PENGASSAN ta tafi idan har tana ganin an tauye haƙƙin mambobinta da matatar mai ta Dangote ta kora maimakon daukar matakin yanke samar da mai.
"Ina ganin PENGASSAN ta wuce gona da iri domin Matatar Dangote, matata ce mai zaman kanta da aka zuba biliyoyin daloli," in ji Sanata Ndume.
Gwamnatin Najeriya ce dai ta shiga tsakani har aka samu maslaha ƙungiyar PENGASSAN ta janye yajin aikinta na kwana uku da ta soma a ranar Litinin 28 ga watan Satumba.









