Antony zai fuskanci Real Madrid bayan soke jan kati

Antony

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

An soke jan katin da aka bai wa ɗan wasan Manchester United, Antony mai buga wasannin aro a Real Betis.

Kenan zai fuskanci Real Madrid a wasan La Liga ranar Asabar, bayan da aka soke jan katin da aka yi masa.

An bai wa ɗan ƙwallon tawagar Brazil jan kati a wasan da Betis ta yi nasara 2-1 a kan Getafe a karshen mako.

Tun farko an dakatar da shi wasa ɗaya, daga baya Betis ta ɗaukaka karar da aka soke jan katin.

Antony ya ci ƙwallo uku ya bayar da biyu aka zura a raga a wasa biyar, tun bayan da ya koma Real Betis a cikin Janairu kan yarjejeniyar zuwa karshen kakar nan.

United ta sayi ɗan wasan daga Ajax kan £85m a 2022, amma ƙwallo 12 ya ci wa ƙungiyar Old Trafford a karawa 96 da ya yi mata.

Betis, wadda take ta bakwai a teburin La Liga, za ta karɓi bakuncin Real Madrid a gasar La Liga a Estadio Benito Villamarin ranar Asabar.