United da Liverpool na harin Gomes, Chelsea na son Rowe

Asalin hoton, Getty Images
Manchester United da Liverpool sun fara tuntuɓa kan yiwuwar ɗaukar ɗan wasan Wolves da Brazil Joao Gomes, 25, bayan rashin nasara komawarsa Atletico Madrid. (Globo - in Portuguese)
Chelsea ta fara tattaunwa da wakilan ɗan wasan Bologna da Ingila Jonathan Rowe, inda ɗan wasan Argentina Alejandro Garnacho, ke shirin barin ƙungiyar. (Il Resto del Carlino - in Italian)
Sporting Kansas City na harin ɗaukar dan wasan Masar Mohamed Salah, bayan da Liverpool ta bashi damar tariya ƙungiyar da ya ga dama, bayan da kwantaraginsa da su ya ƙare. (Athletic)
Ƙungyoyin Ingila masu yawa ciki har da Coventry City da West Ham na sa ido kan dan wasan Bodo da Glimt Patrick Berg, saboda irin rawar da yake takawa a gasar cin kofin duniya da ake bugawa a ya ke wakiltar ƙasar sa. (Teamtalk)
Everton na son daukar dan wasan Ingila da Newcastle United Jacob Murphy, wanda kwantaraginsa ya rage masa shekara guda ta ƙare. (Talksport)
Real Madrid ta shirya wani zama da Vinicius Jr domin kamala sabunta kwataranginsa da ƙungiyar, wasu daga cikin dalilan na taron kuma ana cewa suna duba yiwuwar siyar da ɗan wasan Brazil ɗin. (AS - in Spanish)
Paris St-Germain ta fasa ɗaukar ɗan wasan Barcelona da Sipaniya Ferran Torres, Bradley Barcola, da ke barin ƙungiyar a wannan kaka. (L'Equipe - in French)
Barcelona ta kamala cimma yarjejeniya da Borussia Dortmund wajen ɗaukar ɗan wasan Jamus Karim Adeyemi. (Marca - in Spanish)
Wakilan ɗan wasan Roma Matias Soule na tattaunawa da Sunderland da Fulham, kan yiwuwar ɗaukar dan wasan dan ƙasar Ajantina. (Corriere dello Sport - in Italian)
Tsohon dan wasan Hull City Oscar Zambrano, zai koma ƙungiyarsa daga Maribor da yake taka leda a masatyin dan wasan aro. A 2024 ne dai aka dakatar da dan wasan na wani taƙaitacen lokaci saboda zargin ta'amali da ƙwayoyi. (Hull Daily Mail)
Notthingham Forest ta tuntuɓi Fiorentina kan yiwuwar daukar ɗan wasanta Dodo. (Firenze Viola - in Italian)
Fulham ta amince da ɗaukar ɗan wasan Celtic Erskine Rennie, idan ake sa ran ɗalibin makarantar koyar da ƙwallon ƙafa ta Scouthland kan fam dubu 100, a matsayin diyya. (Sky Sports)











