KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 12/07/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Lahadi 12 ga watan Yulin 2026.

Taƙaitattu

  • Iran ta sanar da kai hare-hare kan sansanonin sojin Amurka biyar a yankin Gabas ta Tsakiya
  • Tsohon sarkin Qatar Sheikh Hamad bin Khalifa Al Thani ya rasu
  • Iran da Oman sun tattauna kan gudanar da zirga-zirgar Jirage a mashigar Hormuz
  • Za mu tsananta martaninmu idan hare-haren Amurka da saɓa alƙawurra suka ci gaba - Iran
  • Tarihin yadda aka assasa rundunar sojin Najeriya da Hausawa 18 a Legas
Skip Bidiyo and continue reading
  • xxx
  • Nigeria
  • xxx
  • Davido
  • xxx
  • Zanga-zanga a aAfirka ta Kudu
  • xxx
  • Ummulkhairi Aliyu
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • Arsenal
  • xxx

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida da Isiyaku Muhammad

  1. INEC ta ƙara wa’adin miƙa sunayen ƴan takarar zaɓen 2027

    ....

    Asalin hoton, INEC/X

    Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya (INEC) ta ƙara wa’adin da ta bai wa jam’iyyun siyasa domin miƙa sunaye da takardun ’yan takarar da za su fafata a zaɓen shugaban ƙasa da na Majalisar Dokoki na 2027.

    A cewar hukumar, sabon wa’adin zai ƙare ne da tsakar daren ranar Talata, 14 ga Yuli, maimakon ranar 11 ga Yuli da aka tsara tun farko.

    INEC ta bayyana cewa ta ɗauki matakin ne bayan ƙungiyar jam’iyyun siyasa ta IPAC ta buƙaci a ƙara lokaci saboda wasu jam’iyyu ba su kammala saka bayanan ’yan takararsu a shafin hukumar ba.

    Hukumar ta buƙaci jam’iyyun siyasa su yi amfani da wannan dama wajen kammala duk bayanan da ake buƙata kafin wa’adin da aka sabunta ya cika.

  2. Oman ta yi allawadai da harin Iran a ƙasarta

    Ƙasar Oman ta yi allawadai da harin jiragen sama marasa matuƙa da Iran ta kai a yankin lardin Musandam, kamar yadda kamfanin dillancin labaran ƙasar ya ruwaito.

    A wata sanarwa da aka wallafa, Oman ta bayyana cewa tana matuƙar tir da harin, tare da jaddada cewa ta ɗauki dukkan matakan da suka dace domin kare tsaron ƙasar da mazaunanta.

    Wannan na zuwa ne bayan rundunar Juyin Juya Halin Iran (IRGC) ta ce ta kai wani "harin ba-zata mai ƙarfi" kan wuraren Amurka da ke tashar Duqm da ke Oman.

    Lamarin ya faru ne sa'o'i kaɗan bayan ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araqchi, ya gana da takwaransa na Oman a Muscat domin tattauna yadda za a gudanar da zirga-zirga da safarar jiragen ruwa a mashigar Hormuz.

    A wata sanarwa ta daban, IRGC ta zargi Amurka da matsa wa Oman lamba domin karkatar da wasu jiragen ruwa zuwa wata hanya da ta kira "ba bisa ƙa'ida ba" a kudancin mashigar Hormuz, tana mai cewa rundunar ruwan Iran ta dakatar da wannan yunkuri

  3. Rukuni na shida na ƴan Najeriya da aka kwashe daga Afirka ta Kudu sun isa Legas

    .....

    Asalin hoton, Getty Images

    Wasu ’yan Najeriya 40 da aka kwaso daga Afirka ta Kudu sun isa filin jirgin saman Legas, wanda ya kai jimillar mutanen da aka dawo da su a rukuni na shida zuwa 1,174.

    Hukumar ’Yan Najeriya Mazauna Ƙasashen Waje (NiDCOM) ta ce mutanen sun isa ne cikin wani jirgin haya.

    Waɗanda aka kwaso sun nuna godiyarsu ga Shugaba Bola Tinubu bisa amincewa da dawo da su cikin gaggawa, tare da yabawa duk masu ruwa da tsaki da suka taimaka wajen gudanar da aikin.

    NiDCOM ta ce gwamnatin Jihar Imo ta bai wa mutanen jihar da suka dawo tallafin naira miliyan ɗaya kowannensu, yayin da kamfanin MTN ya ba su layukan waya da data kyauta tare da alƙawarin tura naira 100,000 ga kowane mutum.

    Haka kuma, gwamnatocin jihohin Edo da Delta da wasu ƙungiyoyi sun sanar da shirye-shiryen tallafa wa waɗanda suka dawo gida.

  4. Sanata Lindsey Graham na jam'iyyar Republican kuma aminin Trump ya rasu

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Sanata mai wakiltar jam'iyyar Republican daga jihar South Carolina a Amurka, Lindsey Graham, ya rasu yana da shekaru 71 bayan wata gajeriyar jinya.

    Ofishinsa ne ya sanar da rasuwarsa a cikin wata sanarwa da aka fitar da yammacin ranar Asabar.

    Graham ya shafe fiye da shekaru ashirin yana aiki a Majalisar Dattawan Amurka, inda ya kasance ɗaya daga cikin fitattun 'yan Republican kuma aminin shugaban ƙasar Amurka Donald Trump.

    Marigayin ya yi fice saboda tsattsauran ra'ayinsa kan manufofin harkokin waje, musamman game da Iran.

    Ya kasance mai goyon bayan matakan matsin lamba kan Tehran, ciki har da ƙaƙaba ƙarin takunkumai da kuma ɗaukar matakai masu tsauri kan shirin nukiliyar ƙasar da ayyukanta a yankin Gabas ta Tsakiya.

    Rasuwar Lindsey Graham ta girgiza harkokin siyasar Amurka, inda shugabanni da abokan aikinsa suka fara aikewa da saƙonnin ta'aziyya.

    Ana kallonsa a matsayin ɗaya daga cikin fitattun sanatoci masu tasiri a jam'iyyar Republican, kuma wanda ya taka rawa sosai a manufofin tsaron Amurka da dangantakarta da ƙasashen duniya.

  5. Senegal ta kori kocinta bayan ficewa daga gasar Kofin Duniya

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Senegal (FSF) ta sanar da fara aikin sallamar kocin ƙasar, Pape Thiaw, da ma'aikatansa bayan ficewar Senegal daga gasar Kofin Duniya ta 2026.

    Matakin ya biyo bayan rashin nasarar ƙungiyar ta kai wa zagaye na 16 bayan ta sha kashi a hannun Belgium da ci 3-2, duk da cewa ta fara wasan da ci 2-0.

    FSF ta ce an yanke shawarar kawo ƙarshen kwangilar Pape Thiaw da ma'aikatansa ne a wani taron kwamitin zartarwa da aka gudanar ranar Asabar, wanda ya duba sakamakon da ƙungiyar ta samu a gasar.

    Hukumar ta kuma ɗora wa shugabanta, Abdoulaye Fall, alhakin sanar da kocin hukuncin a hukumance tare da jagorantar wani sabon shiri na sake fasalin manyan ƙungiyoyin ƙwallon ƙafar ƙasar.

    Ana sa ran Abdoulaye Fall zai yi wa manema labarai bayani a Dakar ranar Litinin kan dalilan ɗaukar wannan mataki da kuma shirye-shiryen da hukumar ke yi domin farfaɗo da ƙwallon ƙafar Senegal, wadda kafin fara gasar ake hasashen za ta kasance ɗaya daga cikin ƙasashen Afrika masu fafutukar lashe kofin.

  6. Za mu tsananta martaninmu idan hare-haren Amurka da saɓa alƙawurra suka ci gaba - Iran

    ....

    Asalin hoton, Tasnim news agency

    Kakakin Majalisar Dokokin Iran, Mohammad Bagher Qalibaf, ya yi gargaɗin cewa Tehran za ta ƙara tsananta martaninta idan hare-haren Amurka suka ci gaba ko kuma idan ba a cika alƙawurran da aka ɗauka ba.

    A wani saƙo da ya wallafa a shafin X, ya ce “zaman yarjejeniyoyin da bangare ɗaya kawai ke ɗaukar nauyi ya ƙare.”

    Qalibaf ya bayyana cewa Iran ta sha kira ga sauran ɓangarori su mutunta alƙawurra da wajibansu, yana mai cewa duk wanda ya ƙi yin hakan dole ne ya fuskanci sakamakon abin da ya aikata.

    Tare da saƙon nasa, ya wallafa wani ɓangare na sashe na biyar na takardar yarjejeniyar Islamabad, wanda ya jaddada gudanar da harkokin mashigar Hormuz bisa ga tsare-tsaren Iran.

    Kalaman nasa na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun takun-saƙa tsakanin Iran da Amurka, tare da ƙarin fargaba game da tsaro da zirga-zirgar jiragen ruwa a yankin.

  7. Iran ta harba mana makaimai masu linzami uku - Jordan

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Sojojin Jordan sun sanar da cewa makamai masu linzami uku da aka harba daga Iran sun faɗo a wasu sassan ƙasar da safiyar Lahadi.

    A cikin wata sanarwa, wata majiya ta soja ta ce makaman sun sauka ne a wurare daban-daban na masarautar Jordan, amma babu wanda ya rasa ransa ko ya jikkata sakamakon lamarin.

    Majiyar ta ƙara da cewa ɓarnar da aka samu ta takaita ne ga ƙananan lalacewar kadarori kaɗai.

  8. Iran da Oman sun tattauna kan gudanar da zirga-zirgar Jirage a mashigar Hormuz

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Iran, Esmail Baghaei, ya ce tattaunawar da ministan harkokin wajen ƙasar Abbas Araqchi ya yi da jami'an Oman a Muscat ta mayar da hankali ne kan yadda za a gudanar da zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigar Hormuz.

    Baghaei ya bayyana cewa tawagogin ƙwararru na fannin shari'a da fasaha daga ƙasashen biyu sun halarci tattaunawar, inda suka yi musayar ra'ayi kan tabbatar da tsaro da lafiyar zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigar.

    Ya ce an tattauna batutuwan da suka shafi mutunta 'yancin mallaka na ƙasashen biyu da ke gaɓar mashigar, da kuma bin dokokin ƙasa da ƙasa, tare da tanade-tanaden sashe na biyar na Yarjejeniyar Fahimtar Juna ta Islamabad.

    Baghaei ya ƙara da cewa Iran ta jaddada cewa duk wani sabon tsari na gudanar da zirga-zirga a mashigar Hormuz ya kamata ya kasance sakamakon shawarwari tsakanin Iran da Oman.

  9. Tsohon sarkin Qatar Sheikh Hamad bin Khalifa Al Thani ya rasu

    ....

    Asalin hoton, Reuters

    Gwamnatin Qatar ta sanar da rasuwar tsohon sarkin ƙasar, Sheikh Hamad bin Khalifa Al Thani, yana da shekaru 74 a duniya.

    Sheikh Hamad ya jagoranci harkokin mulkin Qatar daga shekarar 1995 zuwa 2013, kuma ana kallonsa a matsayin ɗaya daga cikin manyan masu gina Qatar ta zamani.

    A lokacin mulkinsa, ƙasar ta samu gagarumin ci gaban tattalin arziki, wanda ya taimaka wajen ɗaga darajar Qatar a idon duniya.

    Haka kuma, a shekarar 1996 ne aka ƙaddamar da tashar talabijin ta Al Jazeera bisa umarninsa, lamarin da ya sanya kafar yada labaran ta zama ɗaya daga cikin shahararrun kafofin watsa labarai a duniya.

    Rasuwarsa ta jawo alhini a Qatar da ma sauran sassan duniya, inda ake tuna irin rawar da ya taka wajen sauya fasalin ƙasar.

  10. Iran ta sanar da kai hare-hare kan sansanonin sojin Amurka biyar a yankin Gabas ta Tsakiya

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Iran ta ce ta kai hare-hare kan sansanonin sojin Amurka guda biyar da ke Oman, Jordan, Kuwait, Bahrain da Qatar, a wani mataki da ta bayyana a matsayin martani ga hare-haren da Amurka ke kai wa yankunan kudancin ƙasar.

    A cikin wata sanarwa, rundunar juyin juya halin Iran ta ce rundunar sararin samaniyarta ta kai hari kan cibiyoyin kayan aikin jiragen ruwa masu ɗaukar jiragen yaƙin Amurka da kuma wuraren man fetur a tashar jiragen ruwa ta Duqm da ke Oman.

    IRGC ta kuma bayyana cewa ta yi amfani da makamai masu linzami wajen kai harin kan muhimman cibiyoyin soja da kayayyakin more rayuwa a sansanin sojin sama na Prince Hassan da ke Jordan.

    Iran ta ce hare-haren wani ɓangare ne na martanin da take mayarwa kan abin da ta zargi Amurka da aikatawa na "cin zarafin soja", yayin da ake ci gaba da samun tashin hankali a yankin Gabas ta Tsakiya.

    Har yanzu dai babu wata sanarwa daga hukumomin Amurka, Kuwait, Bahrain ko Qatar kan waɗannan iƙirare.

  11. Assalamu alaikum

    Masu bibiyar shafin labaran kai tsaye na BBC Hausa,barkanmu da wannan safiya ta ranar Lahadi.

    Kamar kodayaushe, za mu kawo maku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Aisha Babangida ce ke fatan kasancewa da ku a daidai wannan lokacin.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na facebook da X da kuma whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.

    Ku kasance tare da mu.