Tarukan addini 5 mafiya girma a duniya

Wani cincirndon ƴan ƙsar Turkiyya a lokacin kallon ƙwallo a gasar Cin Kofin Duniya ta 2026

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Usman MINJIBIR
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 5

Addinai da al'adu a faɗin duniya na gudanar da taruka daban-daban, inda miliyoyin mabiya addini ko wata mazhaba ko kuma wata al'ada ke haɗuwa a wuri guda domin bikin.

Mafiya lokuta ana irin waɗannan tarukan ne shekara-shekara wani abu da ke bai wa masu son halartar taron yin tanadi walau dai na kuɗin tafiya ko guzuri.

A yanzu haka akwai taruka manya guda biyar da suka fi kowanne samun taron jama'a a duniya inda kuma uku daga cikinsu na mabiya addinin Musulunci ne sai kuma guda biyu na mabiya addinin Hindu da Yahudanci.

Duk da cewa jerin tarukan biyar ba su zo a jerin da za mu kawo muku ba, ko a kundin bajinta na Guinennes ba amma kuma sun bayyana a ɗaiɗaikuwa, inda muka yi amfani da alƙaluman wajen jerantawa.

1 - Maha Kumbh Mela - Indiya

Mabiya Hindu sun yi imanin cewa wannan yana tsarkake su daga zunubai kuma yana kawo ceton ruhi.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mabiya addinin Hindu a daya daga cikin kogunan da suke yin wankan tsarki.

Wannan shi ne taro mafi girma a duniya da mabiya addinin Hindu ke gudanarwa a duk shekara a ƙasar India.

Ana ƙiyasta cewa aƙalla mutane miliyan 120 na halartar taron amma kuma alƙaluman na sauyawa, kamar yadda hukumar ƙiddiga ta Uttar Pradesh ta bayyana.

Misali taron da aka gudanar a 2013 ya samu mahalarta kimanin miliyan 120, inda na 2025 kuma ya samu mahalarta kusan miliyan 670 wanda ya sa taron ya zama ɗaya daga cikin manyan tarukan jama'a a tarihin duniya.

Ana gudanar da Maha Kumbh Mela sau ɗaya a cikin shekara 12. Ana shirya shi bisa tsarin ilimin taurari na addinin Hindu, kuma wurin yakan sauya tsakanin manyan wuraren ibada huɗu na mabiya addinin:

  • Prayagraj
  • Haridwar
  • Nashik
  • Ujjain

Mafi shahara kuma mafi girma daga cikinsu shi ne na Prayagraj, inda masu inada ke taruwa a kogunan Ganges da Yamuna da Saraswati domin yin wanka na ibada.

Mabiya Hindu sun yi imanin cewa wannan yana tsarkake su daga zunubai kuma yana kawo ceton ruhi.

Wani mabiyin addinin Hindu a taron Maha Kumbh Mela

Asalin hoton, Getty Images

2 - Tattakin Arba'in - Karbala, Iraqi

Aƙalla mutum miliyan 20 zuwa 30 ne ke halartar taron tattakin Arba'in a Karbala.

Asalin hoton, Getty Images

Wannan ne taro mafi girma na biyu a duniya inda mabiya mazhabar Shi'a kan taru a garin Karbala a kwanaki 40 na alhinin kisan Sayyidina Hussaini, jikan Annabi Muhammad (SAW).

An kashe Imam Husaini bn Ali (AS) a ranar 10 ga Muharram, shekara ta 61 bayan Hijira a filin Karbala da ke ƙasar Iraki ta yanzu. Wannan rana ita ce ake kira Ashura.

Alƙaluma daga Karbala sun nuna cewa mutum miliyan 20 zuwa 30 ke halartar wannan alhini a duk ranar 20 ga watan Safar - wata na biyu a addinin Musulunci.

Duk da cewa alƙaluman na sauyawa a duk shekara amma alƙaluma sun nuna cewa mutum miliyan 21 ne suka halarci taron a 2022, inda kuma a 2017 aka samu halartar mutum miliyan 30, kamar yadda hukumomin Al-Abbas Holy Shrine da Imam Hussaini Holy Shrine suka fitar.

Da yawa daga cikin mahajjatan suna yin tafiya da ƙafa zuwa Karbala daga garuruwa da ƙasashe daban-daban.

Mahalarta taron Arba'in a Karbala na ɗaga hotunan da ake kira tamsiliyya na Imam Hussain (AS)

Asalin hoton, Getty Images

3 - Bishwa Ijtema - Bangladesh

Musulmai mahalarta "Akheri Munajat" ko kuma addu'ar ƙarshe a taron Bishwa Ijtema na shekara-shekara a Tongi, kusa da Dhaka, Bangladesh, ranar 2 ga Fabrairu 2025.

Asalin hoton, Getty Images

Taron Bishwa Ijtema da ake gudanar da shi shekara-shekara a ƙasar Bangladesh inda aƙalla Musulmi miliyan 5 ke taruwa a Tongi da ke kusa da birnin Dhaka.

Masu shirya taron suna mayar da hankali ne kan gyaran hali da ibada da haɗin kan Musulmi maimakon harkokin siyasa.

Abubuwan da ake yi a taron sun haɗa da:

  • Wa'azi da karatun addini Musulunci domin ƙarfafa imani da kyawawan ɗabi'u.
  • Taron zikiri da addu'o'i na musamman ga al'ummar Musulmi.
  • Tattaunawa kan yadda za a inganta rayuwar Musulunci da yada addini cikin lumana.
  • Haɗuwar Musulmi daga ƙasashe sama da 150, wanda ke ba su damar sada zumunci da ƙarfafa haɗin kan al'umma.
  • Addu'ar ƙarshe (Akheri Munajat), wadda ke zama muhimmin ɓangare na taron kuma tana jawo dimbin mahalarta.
Musulmai na komawa gida a cikin jirgin ƙasa mai cunkoso bayan kammala addu'ar ƙarshe ta Bishwa Ijtema a Tongi, kusa da Dhaka a Bangladesh.

Asalin hoton, Getty Images

4 - Hajj - Makka

Mahajjata sanye da hirami a lokacin gudanar da salla.

Asalin hoton, Getty Images

Aikin Hajji ana yin sa ne a cikin watan Zul-Hijja, wanda shi ne wata na 12 a kalandar Musulunci.

Muhimman ayyukan Hajji suna gudana daga ranar 8 zuwa 13 ga Zul-Hijja a kowace shekara.

Hajji na ɗaya daga cikin rukunan Musulunci guda biyar, kuma wajibi ne ga duk Musulmin da yake da iko ya yi shi aƙalla sau ɗaya a rayuwarsa.

A mafi yawan shekarun baya-bayan nan, Hajji yana tara tsakanin mutum miliyan 2 zuwa 3 daga sassa daban-daban na duniya.

A shekarar 2010, an ruwaito mahalarta kusan miliyan 2.8, sannan a shekarar 2012, mahalarta sun kai miliyan 3,161,573 kamar yadda hukumar ƙididdiga ta ƙasar Saudiyya, GASTAT ta rawaito.

Mahajjata na addu'o'i a kewayen Ka'aba bayan ɗawafi.

Asalin hoton, Getty Images

5 - Western Wall - Jerusalem

Masu ibadar Yahudawa suna gudanar da addu'a a Katangar Yamma kusa da Wilson's Arch a Urushalima.

Asalin hoton, Getty Images

Western Wall ko kuma Katangar Yamma da ke Urushalima a birnin Qudus na ɗaya daga cikin wuraren ibada mafi tsarki ga Yahudawa, kuma yana karɓar kusan baƙi miliyan 5 a tsawon shekara wato mutane miliyan biyar ke ziyartar wurin a tsawon watnni 12 na shekara ba a lokaci guda ba kamar sauran tarukan.

Wurin yana cikin Tsohon Birnin Qudus kuma ana ɗaukar sa a matsayin abin da ya rage daga bangon da ke kewaye da wurin ibadar Yahudawa na Biyu da ake kira da "Second Temple", wanda Romawa suka rushe a shekara ta 70 Miladiyya.

Saboda haka, Yahudawa daga sassa daban-daban na duniya suna zuwa wurin domin yin addu'a da ibada.

Wani mai ibada yana addu'a a Katangar Yamma (Western Wall) da ke Urushalima, Isra'ila, ranar 7 ga Yuni, 2026.

Asalin hoton, Getty Images