Arsenal na shirin bai wa Saka dogon kwantaragi

Bukayo Saka

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Kwantaragin Saka zai ƙare a ƙarshen kakar 2026-27
    • Marubuci, Sami Mokbel
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Babban Marubucin Ƙwallon Ƙafa
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 1

Arsenal na gab da fara tattaunawa da ɗanwasan gefenta Bukayo Saka domin ba shi sabon kwantaragi yayin da ya rage ƙasa da shekara biyu ya ƙare.

Yanzu Saka na jinyar raunin da ya ji tun watan Disamba a karawar da suka doke Crystal Palace, wanda daga baya aka yi masa tiyata.

Amfaninsa ga tawagar ta Mikel Arteta yana da yawa, hakan ya sa kulob ɗin ke shirin ganawa da wakilan ɗanwasan mai shekara 23.

Arsenal na son ta guje wa duk wani rashin tabbas game da tauraron ɗanwasan ta hanyar ba shi kwantaragi mai tsawo.

A 2022 ne ɗan ƙasar Ingilan ya sanya hannu kan yarjejeniyar da ake tunanin ta kai albashin fam miliyan 10 duk shekara.

Amma yarjejniyar za ta ƙare ne a ƙarshen kakar wasa ta 2026-27.

Kafin amincewa da yarjejeniyar, ƙungiyoyi kamar Manchester City sun nuna sha'awarsu a kansa, kuma a yanzu ma ba za a rasa masu son sa ba idan tattaunawa ba ta tafi yadda ya kamata ba da Arsenal ɗin.

Arsenal na ganin ƙoƙarin da take yi a Premier League bisa jagorancin Arteta da kuma ci gaba da zamansu a gasar zakarun Turai za su taimaka wajen tattaunawa da Saka.

Wasan Arsenal na gaba shi ne wanda za ta karɓi baƙuncin Flham ranar 1 ga watan Afrilu.

Sauran 'yanwasan da ke da muhimmanci sosai a kulob ɗin kamar William Saliba da Gabriel Magalhaes, su ma kwantaraginsu zai ƙare ne a ƙarshen kaka mai zuwa.