PSG ta yi waje da Liverpool daga Champions League

Champions League

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Paris St Germain ta fitar da Liverpool daga Champions League ranar Talata a Anfield a bugun fenariti ta kai kwata fainal.

A wasa na biyu zagayen ƴan 16 da suka kara a Anfield, PSG ce ta ci ƙwallo ta hannun Ousmane Dembele a minti na 12 da fara wasan.

Hakan suka kammala karawar har da karin lokaci, amma ba a farke ƙwallon ba, kenan kowacce tana da 1-1 gida da waje da suka fuskanci juna.

A makon jiya Liverpool ta je Faransa ta yi nasara 1-0, wadda ta ci ƙwallon ta hannun Harvey Elliot daf da za a tashi daga karawar.

Bayan da aka yi karin lokaci a Anfield ranar Talata, daga nan aka je bugun fenariti, inda PSG ta kai kwata fainal da cin 4-1.

Darwin Nunez ne ya fara kasa ci wa Liverpool fenariti da kuma Curtis Jones, kuma Jones ya zama ɗan Ingila na biyu da ya ɓarar da fenariti a Champions League bayan John Terry a wasan karshe a 2008.

PSG za ta buga wasan zagayen gaba da duk wadda ta yi nasara tsakanin Club Brugge da Aston Villa da za su kara ranar Laraba.

Liverpool tana da damar lashe Carabao Cup ranar Lahadai 16 ga watan Maris, wadda za ta fafata da Newcastle a wasan karshe a Wembley.

Daga nan Liverpool za ta kara da Everton a Premier League ranar Laraba 2 ga watan Afirilu, wadda take ta ɗaya a kan teburi da tazarar maki 15 tsakani da Arsenal ta biyu.

Ita kuwa PSG mai shirin lashe Ligue 1 na bana, za ta karɓi bakuncin Marseille ranar Lahadi 16 ga watan Maris.