Ko samamen da FBI ta kai gidan Trump zai tunzura shi?

Donald Trump

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Irin ruwan martanin da ya rika kwararowa daga magoya bayan Donald Trump abu ne da daman za a yi tsammani wanda masu lura da al'amura ka iya cewa sun san a rina wai an saci zanin mahaukaciya.

Ba ta yadda za a yi a ce daman 'yan ga-ni-kashe-nin tsohon shugaban za su kawar da kai ba za su harzuka ba sakamakon wannan sumame da jami'an hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka FBI suka kai gidansa.

Abu ne da za a ce tamkar faduwa ta zo daidai da zama ko kuma an jefi mai son kuka da kashin awaki.

Domin abu ne da aka sani yadda Trump a kodayaushe yake son ya nuna wa Amurkawa ko kuma ma duniya cewa babu wani jigon siyasa da ake yi wa kutungwila ko bi-ta-da-kulli kamar shi.

A zahirin gaskiya samamen na hukumar ta FBI kusan ya taimaka wajen tabbatar da ikirarin da Trump din ke yi na tsanar da yake cewa ana nuna masa a kasar.

Idan ka saurari irin maganganu da korafe-korafen da ke fitowa daga bakin magoya bayansa, za ka ga yadda suke zargin yadda gwamnati ke wuce gona da iri a ganinsu wurin gallaza wa gwanin nasu.

Marco Rubio, dan majalisar dattawa na jam'iyyar Republican daga Florida mai sukan lamirin Trump ne da ya juye ya koma mai goyon bayansa, ya kwatanta abin da hukumar ta FBI ta yi da abin da muka saba gani na faruwa a kasashen duniya matalauta da ke karkashin mulkin kama-karya na Gurguzu.

Kristi Noem, gwamnar jihar South Dakota, wadda tun asali take 'yar ga-ni-kashe-nin Trump, ta kira samamen bai wa FBI makami.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Hukumar da ta ce daman tana ci wa Trump dinddige tun yana dan takara har ya zama shugaban kasa da kuma yanzu da ya zama tsohon shugaban kasa ba ta kyale shi ba.

Akwai alamar ingiza magoya baya a nan ma, kamar dai a can baya, Mista Trump yakan ce idan aka gallaza masa, to kusan ana yi wa magoya bayansa barazana ne.

Shi ne gwaninsu

Kalamai ne na nuna bangaranci da aka saba ji daga masu zaben Trump:

''Farautarsa da suke, kamar farautarmu suke.''

Wannan na nuna mana yadda samamen na FBI ya sauya salon siyasar Amurka.

Da farko dai zai karfafa wa magoya bayan Trump gwiwa su fita sosai a zaben rabin wa'adi na watan Nuwamba.

Sannan 'yan jam'iyyar Republican masu goyon bayan Trump na amfani da batun wajen tara kudin yakin neman zabe ga 'yan takarar da Trump ya mara wa baya.

Karara sun dauki abin a matsayin wata hanya ta tara kudade. Haka kuma batun ya tilasta wa 'yan Republican wadanda a baya suke nuna hamayya ga Trump su sauya shawara su koma wurinsa.

Magoya bayan Trump

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Magoya bayan Trump sun yi tururuwa zuwa gidansa na Mar-a-Lago bayan da labarin sumamen na FBI ya bayyana

Hatta gwamnan Jihar Florida Ron DeSantis, wanda ake yi wa kallon na gaba-gaba da zai nemi yi wa Republican takara idan tsohon shugaban ya ce ba zai nema ba a 2024, cikin hanzari ya fito ya soki sumamen na FBI.

Dukkanin wadannan abubuwan ba abin da suke yi face karfafa wa Trump gwiwa ya fito ya sake neman takarar shugabancin kasar.

Kamar yadda miliyoyin magoya bayansa a fadin kasar ke ta hankoron ganin ya fito ya yi.

Fitowa fili ya bayyana aniyarsa ta sake neman takara ta daburta lissafin wasu daga cikin masu tsara dabaru na jam'iyyar Republican, wadanda ke fargabar cewa ta mayar da tsohon shugaban gefe, wanda har yanzu yake raba kan 'yan jam'iyyar, a matsayin wani babban mai tasiri a zaben rabin wa'adin wand yke da matukar muhimmanci.

Za su so ne su mayar da hankali a kan matsalar hauhawar farashi da kuma koma-bayan tattalin arzikin da Amurkar ke ciki.

Su kuwa 'yan Democrat sumamen na FBI a gidan Trump na Mar-a-Lago yana da hadarinsa na daban.

Bayan zaburar da magoya bayan Jam'iyyar Republican, lamarin ya kuma dauke hankalin jama'a daga irin nasarar da 'yan Democrat din suka samu a Majalisa a wannan makon.

Sun amince da samar da tsare-tsare na tallafin tattalin arziki, wadanda suka kama daga harkar kula da lafiya da sauyin yanayi.

Rashin dacewar samamen a daidai wannan lokaci a siyasance ya sa 'yan Democrat musanta zargin da bangaren Trump ke yi cewa fadar gwamnatin kasar ce ta White House ta shirya sumamen.

''Ni dalibar aikin lauya ce, kuma na damu da tsarin doka ta yi aiki a kan kowa, kuma ina son ganin a ce ba Fadar Gwamnati ba ce take tsara wa ma'aikatar Shari'a abin da take yi ba,'' in ji 'Yar majalisar dokoki Madeleine Dean, lauya kuma 'yar jam'iyyar Democrat daga Pennsylvania.

Tana daya daga cikin wadanda suka yi uwa suka yi makarbiya a kan batun tsige Mista Trump karo na biyu bayan tarzomar ginin majalisar dokoki a ranar 6 ga watan Janairu.

A je a dawo dai a wurin yawancin 'yan jam'iyyar Democrat suna ganin Trump shi ne dan takara mafi sauki da suke son fuskanta a zaben 2024.

Wata kuri'ar jin ra'ayin jama'a a da kafar yada labarai ta Fox News ta gudanar a watan Yuni ta nuna cewa kashi 55 cikin dari na masu zabe da suke da rijista ba sa sonsa a matsayin dan takara.

Ana kallonsa a matsayin mai raba kan jama'a kuma 'yan Democrat na ganin abin da ya yi a zaben baya ba zai taimake shi a zabe na gaba ba.

A duk lokacin da ake maganarsa a labarai, suna ganin hakan na taimaka wa 'yan Democrat a fadin kasar.

Har yanzu Mista Trump na raba kan jama'a

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ana daukar Mista Trump a matsayin mai raba kan jama'a a Amurka

Ms Marsh, mai tara dabarun jam'iyyar Democrat ta yi amanna cewa jam'iyyarta za ta samu gagarumar karba a zaben rabin wa'adi na Nuwamba.

Saboda hukuncin Kotun Koli a kan batun hana zubar da ciki da kuma yadda Jam'iyyar Republican ta kasa dora alhakin tarzomar da aka yi a ginin Majalisar Dokoki ranar 6 ga watan Janairu a kan jagoransu.

Ko da ya tsaya takara ko bai tsaya ba, k da ya bayyana aniyarsa ta yin takara kafin zaben rabin wa'adiko kuma bai yi ba, ta wani fannin wannan ba shi ne abu mafi muhimmanci ba.

Bayan sumamen na FBI, mun ga yadda cikin gaggawa shugabannin Republican suka goyi bayansa.

"Wannan lamarin ba wai magana ce a kan Trump ba," in ji Michael Steele, mai sukan lamirin Trump kuma tsohon shugaban kwamitin kasa na jam'iyyar Republican.

"Wannan yanzu ba magana ce ta Trump ya kewaya kasa ya rika babatun karya a kan zabe, da kuma ci gaba da bata mulkin kasa ba.

Yanzu yana da 'yan barandarsa da za su yi masa wannan.

"A wannan bazarar na kewaya sassan Amurka inda na rika tattaunawa da magoya bayan Trump.

Fiye da sau daya na ji su suna cewa yakin basasa zai barke a kasar. Ko a ranar Litinin da daddare a shafukan intanet, an ga yadda yawancin magoya bayan Trump ke cewa matakin na FBI zai kai da haddasa tashin hankali.

Steven Crowder, mai goyon bayan Trump, wanda yake da mabiya miliyan 1.9 a shafukan sada zumunta da muhawara ya rubuta a shafinsa na Twitter cewa: Gobe akwai yaki. Ku yi barcinku ku more.''

Har yanzu zuciyata ta kasa yarda cewa Amurka na cikin hadarin fadawa wani sabon yakin basasa.

To amma wani da y kasance yana bibiyar siyasar 'yan Republican tsawon gomman shekaru, Mr Steele, yana ganin akwai alamun hakan

Ya ce "Da gaske ne.

Wannan ya kasance kusan abin da ke zuciyar 'yan Republican tsawon shekara 10 ko 15.

Trump ya bayar da damar yin hakan ne kawai.

Ya bude fagen. Idan har suka kama mutumin nan da laifi, mutanen nan za su harzuka.''

Abin fatan kawai shi ne. Allah Ya sa lamarin bai kai haka ba, in ji marubucin.