Kudin kirifton da ba a bukatar makamashi mai yawa wajen tara shi

Ethereum co-founder Vitalik Buterin

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Vitalik Buterin, daya daga cikin wadanda suka kirkiro kudin kirifto, ya ce an tsara yin hadakar shekaru da dama da suka wuce
An wallafa

Kudin kirifto na biyu mafi girma, Etherium, yana shirin komawa wani sabon tsari da zai yi amfani da makamashi kasa da kashi daya cikin dari na wanda ake amfani da shi a yanzu.

Tsarin, wanda ake kira The Merge, an yi shi ne don sauya wa masu korafi da ke ganin kudin kirifto na gurbata muhalli. Etherium na amfani da makamashi mai yawa a yanzu.

Sauran kudaden kirifto da suka hada da Bitcoin, za su ci gaba da amfani da makamashi mai yawa.

Vitalik Buterin, daya daga cikin wadanda suka kirkiro kudin kirifto, ya ce hadin na cikin wani bangare da Etherium ke shiryawa tun bayan kaddamar da kudin a 2014, amma an dage hakan lokuta da dama saboda wasu matsaloli.

An kwatanta shi da kamar sake gina tubalin bene yayin da yake tsaye.

Kudin kirifton na kuma tallafa wa wasu kudade har ma da daruruwan miliyoyin dala da kuma sulalla da sauran kudaden intanet na zamani.

Idan wani abu na daban ya faru, hakan zai iya shafar kudin kirifto da manya da kuma kananan masu zuba jari a fadin duniya. Idan kuma tsarin da za a koma yayi kyau, kada masu amfani da kudin su lura da wani canji.

“Abin farin-ciki ne da kuma babban ci gaba. Muna tunanin cewa da wuya abubuwa masu kyau har kashi 100, amma dai wannan hasashe ne,’’ a cewar wani mai bincike kan kudin kirifto, Justin Drake. “Muna da ababen more rayuwa a kasa, wadanda za su ba mu damar ci gaba ko da kuwa wasu cibiyoyin sadarwa sun samu matsala saboda wasu dailai.”

Kwamfutoci sun riga sun fara aiki domin aiwatar da sabon tsarin. Ana kuma sa ran kammala shi nan da ranar Alhamis.

Mene ne hadakar?

Kudin kirifto na Etherium yana da fadin gaske, kuma ba za a iya canja bayanan ba wadanda kuma ke yin rajistar kowace mu’amala da masu amfani da shi ke gudanarwa.

Prima Technologies mining warehouse
Bayanan hoto, Hadakar na tilasta wa ma'aikata a kamfanin Prima Technologies maye gurbin kayan Kirifton su domin fara tara Bitcoin

Zuwa yanzu, an sabunta shi, da kuma tabbatar da cewa an kiyaye ta hanyar amfani da masu aikin sa-kai a fadin duniya da kuma manyan kwamfutoci na zamani, wadanda za a bai wa ladan yin aikin da ba su sabbin tsabar kudi – tsarin da aka fi sani da mu’amalar kudin kirifto.

Ana kiran wannan tsari da Hujjar yin aiki kuma yawancin sanannun kudaden intanet kamar Etherium da Bitcoin da Dogecoin da Litecoin.

Kazalika, rage yawan makamashi na kudin kirifto yana rage adadin tsabar kudi da aka bayar a matsayin lada, kuma kudin na intanet ya ce hakan zai haifar da faduwar tsabar kudi da ke wanzuwa.

Yana da dadin amfani a muhalli

Ba wai rage adadin kwamfutoci da ake bukata kawai hujja ta hannun jari ke yi, yana kuma rage karfin aiki na kwamfutcoi da ake bukata.

Ana iya amfani da kwamfutcoin yau da kullum maimakon wadanda suke da tsada da kuma ke rike wuta da ke dauke da na’urorin sarrafa hoto.

Yana da wuya a gane yawan makamashi da kudin Kirifto ke bukata kafin sarrafa shi a duniya.

Gidauniyar kudin kirifto, ta ce Etherium na amfani da wutar lantarki mai yawa kamar Netherlands a watan Yuni.

Gidauniyar ta kuma ce Hujjar hannun jari zai rage yawan amfani da makamashi daga sa’a 112 na Terrawatt a shekara zuwa 0.01.

Sabon kiyasi da wata kungiya da ke binciken tattalin arzikin kudin digital, Digoconomist, ya nuna cewa an samu raguwar makamashi da ake amfani da shi a kudin kirifto, inda Etherium a yanzu ke amfani Terrawats 82 a shekara.

Me zai faru yanzu da masu tara kudin kirifto?

Hadakar a yanzu zai sanya masu tara kudin kirifto daukar mataki mai wahala.

Ethereum miner Josh Riddet
Bayanan hoto, Wani mai tara kudin kirifto da ke birnin Manchester, Josh Ridett, ya ce yana fatan cewa zai samu riba wajen tara tsabar kudi da darajan shi ba shi da yawa
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Kudin kirifto kan fadi zuwa kasa, lokacin da darajar sulalla ya tashi, wanda kuma ke sanya tara kudin kirifto ya zamanto babu riba a ciki.

Ana samun karuwar matsalar makamashi a sassan duniya da dama, wanda hakan ke rage riba da za a samu.

A yanzu, masu tara kudin kirifto, za su nemi sabon hanyar samun kudi ko kuma sayar da kayakinsu.

A wani kamfanin tara kudin kirifto a Dubai, jami’an kamfanin na zuba jarin dubban daloli domin maye gurbin kwamfutocin da ake amfani wajen samun Etherium da wasu sabbin kwamfutoci kuma masu tsada da ke tara kudin Bitcoin.

"Yana da wahala kwarai, saboda babu wata hujja da ta nuna cewa tsabar kudi sun fi cin kasuwa fiye da kirifto,’’ a cewar mai magana da yawun kamfanin, Ammar Lashkari.

"Za mu ajiye sauran kwamfutocin mu na kirifto, inda za mu nemi wata hanya ta fara tara sulalla, sai dai, ba zai zamanto iri daya ba, don haka ne ma za mu koma tara kudin Bitcoin.’’

A yankin Staffordshire da ke Birtaniya, Ash Andrews na fatan samun riba mai kyau ta hanyar tara tsabar kudi.

"Ina da shakkan hadakar. Lokaci mai kyau ne gare mu yanzu masu tara kudin kirifto, inda yanzu za mu sauya zuwa wani na’uin kudi. Akwai sauye-sauye da dama.’’ In ji Andrews.