Newcastle na zawarcin Mourinho, Barcelona na son Giovani Lo Celso

An wallafa

Barcelona na zawarcin dan wasan tsakiya na Tottenham da Argentina Giovani Lo Celso, mai shekara 27 a matsayin aro a watan Janairu. (90min)

Ana ci gaba da tattaunawa kan cinikin dan wasan tsakiya na Manchester United da Netherlands Donny Van de Beek mai shekara 26 don komawa Eintracht Frankfurt a matsayin aro.(Fabrizio Romano on X)

Shugabannin Newcaste na ci gaba da sha’awar Jose Mourinho a Roma, inda kwantiragin kocin mai shekara 60 zai kare a bazara mai zuwa, duk da cewa kungiyar ta Serie A tana son ta ci gaba da rike shi a matsayin kocinta. (Gazzetta dello Sport - in Italian)

Getafe na fatan sayan dan wasan gaban Ingila Mason Greenwood, mai shekara 22, daga Manchester United amma za su yi riba saboda kashi 20 cikin dari da aka saka a karkashin yarjejeniyar bayar da shi aro ga kungiyar ta La Liga. (Athletic - subscription required)

Arsenal ta yi tayin fam miliyan 17.2 tare da wasu kare-kare ga dan wasan gaban Santos da Brazil mai shekara 20 Marcos Leonardo,. (Fichajes - in Spanish)

Kawo yanzu Juventus na sha’awar daukar dan waaan tsakiya Manchester City da Ingila Kalvin Phillips mai shekara 28 akan aro a watan Janairu.. (Gazzetta dello Sport - in Italian)

Chelsea na son daukar dan wasan gaba na Sporting Lisbon' da Sweden Viktor Gyokeres, mai shekara 25. (Ekrem Konur on X)

Tsohon kocin Wolves da Sifaniya Julen Lopetegui, mai shekara 57, na jan hankalin Crystal Palace da Nottingham Forest. Dan kasar Sifaniyar bai jagoranci wata kungiya ba tun bayan da ya bar Wolves a watan Ogusta.. (Sun)

Mai tsaron bayan Liverpool da Faransa Ibrahima Konate, mai shekara 24, ya soma tattaunawa domin tsawaita kwantaraginsa da Reds, duk da cewa ya na kan tattaunawar komawarsa Paris St-Germain da taka leda. (le10sport - in French)

Sai Sunderland ta yi dagaske a tattaunawar da take yi da Will Still idan tana son ta shawo kan kocin Dan Belgum haifaffen Ingila mai shekara 31 , wanda shi ne kocin Reims. (Telegraph - subscription required)

Borussia Dortmund ta bi sahun Newcastle wajen neman Serhou Guirassy, da ke taka leda a Stuttgart mai shekara kuma dan wasan gaban Guinea Guirassy ya ci kwallaye a gasar Bundesliga ta bana . (Sport Bild - in German)

Wakila Manchester United, da Manchester City da Tottenham da Liverpool na kalllon na wasan tsakiya Middlesbrough da Ingila na yan kasa da 21 Hayden Hackney tare da fatan zai bar kungiyar a bazara mai zuwa. (Mail)