Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ivory Coast za ta cika filaye da 'yan makaranta da 'yan aikin sa kai
Dan kasar Ivory Coast, Ghislain Konan ya ce abin alfari ne da za su karbi bakuncin gasar kofin Afirka a 2024, ya ce za su karbi baki da hannu bibiyu.
Za a fara gasar daga 13 ga watan Janairu a kuma karkare 11 ga watan Fabrairun 2024.
''Zan sanar da kai cewar komai zai wakana kamar yadda aka tsara,'' Konan, wanda yake taka leda a Saudi Arabia ya sanar da hakan a hirar da ya yi da BBC.
''Kasa ce mai maraba da baki da kowa da kowa, kamar yadda muke fada a gida, muna kaunar baki fiye da 'yan kasa.
''Hakika za mu tarbi 'yan kallo, wadanda za su ziyarce mu, haka kuma za mu nuna musu cewar muna kula da baki kuma babbar kasa ce.''
Konan, wanda aka haifa a birnin Abidjan, yana wadan nan kalaman, bayan da gwamnatin Ivory Coast ta ce za ta cika filaye da 'yan aikin sa kai 20,000 da 'yan makaranta a gasar ta cin kofin Afirka.
Gasar da tun farko an tsara yi daga Yuni zuwa Yuli, an mayar da ita daga Janairu zuwa Fabrairun 2024, saboda a kauce yanayin damuna a kasar.
Birnin Abidjan shi ne zai yi amfani da filaye biyu - inda sabon filin da aka gina, Alassane Ouattara Olympic, zai karbi bikin budewa da rufe wasannin.
Yayin da filin Bouake da San Pedro da Korhogo da kuma Yamoussoukro suna cikin wuraren da za a gudanar da gasar.
Wasu filayen za su ci 'yan kallo 20,000, ya yin da filin da ke Abidjan da ake kira Felix Houphouet-Boigny da na Bouake kan ci 'yan kallo 40,000 ya yin da Alassane Ouattara ke daukar 'yan kallo 60,000.